✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yadda abin ya faru – Usman Sakwaya

Sunana Usman Sakwaya mazaunin Unguwar Rijiyar Lemu a Karamar Hukumar Fagge kuma ni dan uwan Ahmed Sakwaya ne.  Abin da ya faru akwai wani da…

Sunana Usman Sakwaya mazaunin Unguwar Rijiyar Lemu a Karamar Hukumar Fagge kuma ni dan uwan Ahmed Sakwaya ne.  Abin da ya faru akwai wani da ake kira Mallah tare suke kasuwanci aka kama shi kusan wata shida, sai suka zo suka ce sun zo su sayi mota ne a hannun Alhaji Garba, aka yi cinikin mota da shi har suka daidaita suka ce, ya zo gobe za su ba shi kudi. Washegari da ya zo sai suka dauko ankwa suka dora wa Alhaji Garba suka tambaye shi ya san Ahmed, sai ya ce bai san Ahmed ba saboda ya rikice sakamakon bai taba shiga irin wannan yanayin ba. Sai suka ce wane ne shugabansu, sai aka kira Alhaji Muhammadu Sambo aka tambaye shi Ahmed ya ce ya san shi yaronsa ne, sai suka ce yana ina? Idan Ahmed ya zo za mu sake ka, sai ya ce bari a kira Ahmed din. Da aka kira shi a waya sai ya ce yana kusa. Da ya zo sai suka ce masa, ka san wani ana ce masa Mallah? Sai ya ce ya san shi, sai suka ce ka zo mu je wasu maganganu za mu yi, amma za a dawo da kai. Bayan sun tafi da shi sai suka tambaye shi akwai kudin da Mallah ya ba shi? Sai ya ce akwai. Sai suka ce nawa ne? Ya fadi kudin. Daga karshe sai suka ce, shi Alhaji Garba motocin da ke hannunsa zai gyara su a sa mai a taho da su, idan ya so in an gama bincike za a dawo da su. Da aka tamye su su wane ne sai suka ce, su DSS ne daga Abuja aka turo su, amma a nan ofishinsu na Gwale idan an gama bincike za a dawo da su, karshe da ake ta kiran wayarsu sai suka fara zage-zage har suka kai ga kashe wayarsu. Tun daga nan babu wani labarinsu sama da shekara daya da wata hudu ke nan.