✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kano ke jefa matafiya cikin kunci da hadari

Ga dukkan alamu, direbobi da fasinjoji masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano ba su jin dadin bin hanyar, sakamon aikin gyara…

Ga dukkan alamu, direbobi da fasinjoji masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano ba su jin dadin bin hanyar, sakamon aikin gyara da ake yi wanda kuma ke sanya jama’a a cikin kunci da jawo hadurra da kan haddasa rasa rayuka.

Mafi yawan direbobin da miniya ta zanta da su, wadanda kuma ke yawan bin wannan hanya sun nemi a gaggauta kammala aikin, domin a cewarsu jama’a na shiga cikin hadari saboda tafiyar hawainiyar da aikin yake yi.

Kafin a fara gyaran hanyar Kaduna zuwa Kano, ga direban da ke son zuwa Zariya daga Kaduna, tafiyar kilomita 82 ce kuma mutum idan ya yi tuki ko gudun kilomita 100 zuwa 120 a awa daya, zai isa Zariya cikin mintoci 40. Amma a yanzu direba ba zai iya kintacen tsawon lokacin da zai isa ba, domin matsalolin da yake gamuwa da su.

A lokacin hanyar na da dadi da saukin bi ga matafiya saboda kyanta da kuma rashin ramuka a dukkan tagwayen hanyoyin amma a ’yan shekarun nan hanyar ta yi matukar lalacewa, inda wasu gadoji da ke hanyar suka lalace kwalta kuma ruwa ya wanke ta sannan ga ramuka munana a tsakiyar titi da kuma gefe, duk sun zaizaye.

Bin hanyar ya zama abin damuwa ga matafiya saboda ramuka da ke janyo yawan kauce-kauce a yayin tuki, domin gudun fadawa cikinsu. Saboda yawan guna-gunin matafiya, Majalisar Zartarwa ta Kasa a watan Disamban 2017, ta amince a ba da kwangilar gyaran hanyar. Sannan wakilan Gwamnatin Tarayya suka kaddamar da fara aikin.

Aikin ya faro daga Abuja zuwa Kaduna, ya wuce Zariya zuwa Kano kuma ya shafi dukkan tagwayen hanyoyin ne. Kudin aikin zai fito ne daga Hukumar Samar da Kudade da Inganta Ayyuka da ke Ofishin Shugaban Kasa, inda za a fitar da Dala miliyan 65 daga asusun Ma’aikatan Samar da Gas ta Kasa, kamar yadda al’amarin ya samu amincewar Kwamitin Tattalin Arziki na Kasa.

An ba da kwangilar ce a kan Naira biliyan 155 ga Kamfanin Julius Berger kuma tuni aka fara aikin, musamman daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya. Da farko jama’a sun yi ta murnar cewa gwamnati ta saurari koke-kokensu kan lalacewar hanyar, to amma sai ga shi gyaran ya zo da nasa matsaloli. An samu sabani kan alkawarin da Shugaban Kamfanin Julius Berger, Wolfgang Goetch ya yi a watan Yunin bara.

Goetch ya ce kamfanin ya samar da wata na’ura ta markade kwalta, wadda ba a taba yin amfani da ita a Najeriya ba. Ya ce tsarin da za su yi amfani da shi zai rage cinkuso a kan hanyar, ba yadda aka saba gani ba idan ana gyara a kan titi. Amma tunda aka fara wannan aiki a watan Yunin 2018, babu abin da ake ji daga wurin matafiya sai korafi.

Masu motoci suna korafin cewa akalla a kullum sai an yi hadari a hanyar saboda yawan karkatar da su da ake yi zuwa hanya daya, maimakon biyu da suka saba bi. Sannan ba a saka alamu a hanyar, da za su nuna irin tafiyar mitar da diraba zai yi. Cinkoson hanya da rashin hakuri na wadansu direbobi kan sa tafiyar da ba ta wuce ta minti 40 ba, yanzu sai a kwashe sa’o’i da dama.

Wani masanin harkar lafiya, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa ya bayyana wa wakilinmu cewa akalla hadurra uku ake yi a kullum a kan hanyar saboda rashin sanya abubuwan da ya kamata kafin fara aikin hanyar.

Daga cikin abubuwan, ya ce ba a samar da jami’i ko manaja da zai rika lura da yadda ake gudanar da hanyar da kuma rashin alama da za ta rika ankarar da matafiya, sannan babu cikakken bayani a kan iya gudu ko tafiyar da direba zai yi a wannan hanya; sai kuma rashin bayani a kan yanayi.

“A wasu kasashe, kafin a fara irin wadannan manyan ayyuka sai an tabbatar da an samar da dukkan matakan da suka kamata a dauka. Amma mu a nan sai dai a mayar da hankali wajen kare rayukan ma’aikata maimakon na matafiya. Shi ya sa duk inda ka ga suna aiki za ka ga ma’aikatansu sanye da kayan leda, rike da jar tuta suna nuna wa direba ya bi a hankali,” inji shi.

Babban Kwamnadan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa da ke Kaduna, Hafiz T. Mohammed, ya yarda da cewa akwai bukatar direbobi su yi amfani da hankalinsu wajen tuki, tare da sanin tafiyar kilomita nawa za su yi a kan wannan hanya.

Ya ce “Idan akwai ababen hawa da yawa a kan hanya, ya fi dacewa ka yi tafiyar kilomita 30 zuwa 40 a awa daya amma abin damuwa shi ne, wadansu direbobin saboda rashin hakuri sai ka ga suna wuce na gabansu ta dama, wanda hakan ya saba wa dokar tuki.”

Wakilinmu ya kuma lura cewa hanyar daga Kaduna zuwa Zariya an raba ta gida shida, kowace da hanyar shiga da fita sai dai duk da ana ci gaba da aiki har yanzu babu inda aka kammala. Sai direba ya kwashe tsawon minti bakwai kafin ya fice daga kowane shinge kuma akan samu yawan ababen hawa wajen fita ko shiga kowane shinge.

Direbobi marasa hakuri sai su yi ta kokarin yanke layi duk kuwa da hanyar ta zama daya da masu shiga da kuma masu fita. Kwamanda Hafiz ya ce an kirkiro da shingayen shida ne saboda a taimaka wajen rage gudu. Ya kara da cewa yawan ababen hawa da ke bin titin Kaduna zuwa Zariya da nufin wucewa wasu yankunan Arewa maso Yamma ko Arewa maso Gabas ko su yiwo Kudu daga can na da yawan gaske.

“Za ka yarda da ni cewa ababen hawa masu yawa su yi amfani da karama ko tsukakkiyar hanya ba za ta ishe su ba. Mun saba yin amfani da tagwayen hanya amma yanzu an dawo da su daya. Saboda haka muke fama da cinkoson ababen hawa, musamman a kwanakin karshen mako saboda mutane sun fi yin tafiya ranar Juma’a, sai kuma masu dawowa ranar Lahadi,” inji shi.

Ya kara da cewa hukumar ta kara yawan ma’aikatanta a Birnin Yero da Dankande da Kwanar Farakwai. Su kuma masu aikin na ci gaba da zuba manyan kayan aiki a hanyar, yayin da ake ci gaba da aiki.

Wakilinmu  ya kuma lura da cewa an saka jami’an FRSC a wasu wurare na musamman a kan hanyar, domin sanya ido a kan yadda direbobi ke tuki. Haka kuma tafiya a hankali da manyan motoci irin su tireloli a kan hanyar na taimakawa wajen kawo cinkoso.

Wani direba a garajen Kawo Kaduna, Malam Hassan wanda a kullum yake bin hanyar zuwa Zariya, ya koka cewa direbobi ba su jin dadin bin hanyar. “Gaskiya ba mu samun sauki wajen bin wannan hanya tunda aka fara gyara, domin da wuya mako ya wuce ba a samu cinkoso ba. ’Yan kwanakin nan ma an samu wani cinkoso tun karfe uku na rana nake kan hanyar amma har sai da asubahin wayewar gari na bar wurin,” inji shi.

Ya ce jami’an FRSC za su taimaka matuka idan suna cire motar da ta lalace a tsakiyar hanya da sauri, domin rashin yin hakan ke janyo cinkoso.

Shi ma wani direban mota a garejin Unguwar Sarki, Abdullahi ya ce muddin ba a kammala aikin titin kafin Disamba ba, za a fuskanci karin matsaloli, domin lokaci ne da jama’a ke yawan yin tafiya.

Shi ma wani direba, Bashir Adam ya ce, “Kusan kullum sai an hatdari a kan wannan hanya. Na ga hadurra kusan biyar a kan hanyar dawowa. Abin kawai sai dai du’a’i da kuma hakuri. Wasu lokutan nakan kwantar wa fasinjoji hankali, musamman masu matsa mini cewa in yi gudu, ina cewa ba mutuwa ake gudu ba sai dai wahala da za a fuskanta idan aka samu hadari,” inji shi.

Shi ma wani direba Suleiman Jaji ya ce a kullum yakan fuskanci cinkoson ababen hawa a kusa da Rigachikun zuwa Birnin Yero. “Wannan waje a kullum muna fuskantar matsala, yana rage mana yawan sawu da muke yi daga Kaduna zuwa Zariya. Kafin a fara wannan aiki, nakan yi sawu uku zuwa hudu da fasinjoji amma a yanzu sawu biyu kacal nake yi kuma hakan na shafar kudin shigar da nake samu a kullum,” inji shi.

Wani fasinja mai suna Johnson Adedire ya ce an dauki lokaci wajen kammala wannan aiki na gyaran hanya. Shi ma wani Shittu Ibrahim ya ce akwai bukatar a kara azama domin a samu a kammala aikin cikin lokaci.

Shi kuma Yunusa Ahmed kira ya yi ga masu motoci su ci gaba da hakuri har a kammala gyaran da ake yi.