✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka ceto Magajin Garin Daura a Jihar Kano  

Jami’an hadin gwiwar tsaro na musamman da ke yaki da masu aikata ta’addanci masu taken,”Operations Puff Adder” tare da rundunar `Ƴansandan Jahar Kano sun yi…

Jami’an hadin gwiwar tsaro na musamman da ke yaki da masu aikata ta’addanci masu taken,”Operations Puff Adder” tare da rundunar `Ƴansandan Jahar Kano sun yi nasarar ceto Magajin Garin Daura Alhaji Musa Uba, wanda aka aka yi garkuwa da shi tun 1 ga watan Mayu 2019, bayan wani hari tare da harbe-harbe da ‘yan bindigar suka yi a lokacin da suka zo sace shi a kofar gidansa da ke cikin garin Daura bayan sallar Magariba.https://www.dailytrust.com.ng/kano-demolishes-house-where-magajin-garin-daura-was-rescued-video.html

Tun daga wannan rana ba’a sake samun kowane irin labari ko rahoto akan halin da yake ciki ba har zuwa safiyar wannan Talata ta wannan mako inda aka samu rahoton kubutarsa ya baiyana daga wajen iyalansa da kuma rundunar Ƴansandan Jahar Katsina ta hannun Kakakin hukumar ‘yan sanda DSP Gambo Isa.

Shi dai Magajin Garin Daura, wanda yake tsohon Kwantarola ne a Hukumar Kwastan ta Kasa, Dan-uwa ga Sarkin Daura Farouk Umar Farouk, sannan kuma suruki ne ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin yana auren Hajiya Bilkisu wadda take ‘ya ce ga Hajiya Rakiya Yayar shi Shugaba Buhari. Kazalika, Dogarin Shugaban Kanal Muhammad Abubakar na auren Fatima ‘yar shi Magajin garin.

Kamar yadda Aminiya ta ci karo da wani rahoto daga Kakakin rundunar `Ƴansanda na Jahar Kano DSP Haruna Abdullahi ya baiyana ta sanarwar da ya bayar a gidan rediyon Tarayya da ke Kano, inda ya ce, jami’an hadin gwiwar sun kai wannan samame ne da misalin karfe 8 na daren Litinin na wannan mako a Unguwar Gangan Ruwa da ke cikin Karamar Hukumar Kumbotso da ke Jahar ta Kano inda kuma suka yi nasarar tseratar da Magajin ba tare da samun ko kwarzane ba. Jami’an kuma sun yi nasarar kama wasu a lokacin da suka kai wannan samamen tare da samun bindigogi da harsasai, kamar yadda Kakakin DSP Haruna Abdullahi ya sanar.