✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gano kokon kan magidanci boye a ckin motarsa

Juma’ar karshe gabanin fara wannan Azumi ta kasance ranar tashin hankali ga iyalan Malam Muhammad Saba, wanda ya bar gidansa da ke Unguwar Second Gate…

Juma’ar karshe gabanin fara wannan Azumi ta kasance ranar tashin hankali ga iyalan Malam Muhammad Saba, wanda ya bar gidansa da ke Unguwar Second Gate da ke Garin Suleja a Jihar Neja a ranar ba tare da dawowa ko jin duriyarsa ba.

Marigayin wanda gabanin rasuwarsa ma’aikaci ne a sashin tattara bayanan filaye da taswirarsu na Abuja (AGIS), ’yan sanda sun garzaya wajen iyalansa, matar aure daya da kuma ’ya’ya 4 washegari ranar Asabar da safe, inda suka sanar da su labarin gano kokon kansa a cikin motarsa da ya bar gidan da ita a ranar da lamarin ya faru.

Lokacin da wakilinmu ya garzaya gidan a ranar Lahadin da ta gabata, ya tarar da gidan a garkame inda makwabta suka sanar da shi cewa an wuce da iyalan zuwa gidan iyayen marigayin da ke garinsu na Bida bayan zaman makoki a ranakun farko na aukuwar lamarin. Aminiya ta zanta da wani makwabcin marigayin mai suna Malam Ndana Muhammad, inda ya ce ko a ranar ta Juma’a ya halarci Sallar Juma’a da kuma ta La’asar tare da marigayin, kafin washe gari ’yan sanda suka zo gidansa da labarin abin da ya faru, kasancewarsa makwabci ga marigayin.

“Bayan nan sun dauke ni zuwa babban ofishinsu na A dibision don in tantance ko shi ne, inda suka fito da kokon kansa daga cikin wani buhu, da suka ce sun gano a bayan motarsa bayan sun yi kicibis da wanda ake zargi da hannu a kisan, yana tuka motar marigayin sannan suka tsayar da shi bai tsaya ba,” inji shi.

Aminiya ta samu labarin cewa wani dan uwan marigayin ya ga dan uwan nasa yana tuka motar ta kusa da babban asibitin garin tare da wani zaune a kujerar gaba a yammacin ranar Juma’ar.

Babban jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Muhammad Dan-Inna wanda ya fitar da sanarwa a ranar Asabar da ta gabata, ya bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Samuel, wanda ya bayyana shi a matsayin aboki a gare shi. Ya yi bayanin cewa motar sintiri ta ’yan sanda ta yi kokarin tsaida mutumin da ke tuka motar marigayin samfurin Toyota Camry tare da wasu a kusa da Garin Lambata da ke kan hanyar Suleja zuwa Minna, amma sai wadanda aka tsayar din suka yi harbi ga bangaren ’yan sanda.Yan sandan sun mayar da martani, inda suka samu nasarar harbe Samuel a kafa sannan bayan sun bincika motar sai suka gano kokon kan marigayin a ciki. A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe marigayin tare da jefar da gangar jikinsa a wani waje a Jihar Nassarawa. Daga bisani wanda ake zargin ya mutu a Asibitin Suleja, inda aka garzaya da shi.

Tuni dai aka yi jana’iza tare da binne kokon kan marigayin a makabartan Suleja tun a ranar ta Asabar, kamar yadda wasu makusantan marigayin suka tabbatar wa da wakilinmu.