Da Dumi Dumi

Yadda aka gudanar da bikin Zango da Maryam

A ranar Asabar da ta gabata ne aka daura auren fitaccen jarumin fina-finan Hausa Adam A Zango da kuma Nana Maryam Abdullahi Yola a kan sadaki Naira dubu 50.
An daura auren ne a masallacin Juma’a na ‘yan Izala da ke Lubge a Abuja da misalin karfe 2:20 na rana.
A lokacin da limamin masallacin yake daura auren ne ya fara gudanar da tambayoyi ga waliyyin amarya, kafin waliyyin amarya ya fara amsawa ne sai tawagar ango da ta kunshi Ali Nuhu da Abdul’aziz dan Small da Murtala Boloko da sauransu suka shigo, hakan ya sanya aka jinkirta ci gaba da daura auren, inda kuma yaran da suka yi musu rakiya suka ci gaba da ihu da kuma tafi, sai da aka dauki lokaci kafin aka ci nasarar hana yaran ihu.
Daga nan sai aka sama wa ango da Ali Nuhu da sauran ‘yan tawagarsu wurin zama kafin aka ci gaba da daura auren.
Hakan ya sanya limamin masallacin ya sake gabatar da tambayoyi inda kuma waliyyin amarya Malam Adamu ya amsa su. Ya  ce: “Maryam budurwa ce, ta samu tarbiyya ta kwarai, lafiya kalau take, domin babu wani abu na ciwo da yake damunta.” Wakilin ango Adam A Zango shi ne Alhaji Shehu Sulaiman ya ce ango zai iya rike amana kuma ba shi da wani abu na ciwo da ke damunsa. Daga nan aka daura aure kowa ya kama gabansa.
A ranar Asabar din aka tafi da amarya gidan mijinta da ke Kaduna.
Idan ba za a manta ba dai a makon jiya mun rawaito za a daura auren a ranar Juma’a 14 ga watan Yuni, 2013, daga baya kuma aka dage ba tare da an bayyana dalilin hakan ba.
Haka dai a ranar Juma’ar da ta gabata an ce bangaren ango za su shirya wata kwarya-kwaryar liyafa a garin Kaduna, amma kuma daga baya ita ma aka daga, sai dai wata majiya ta kusa da angon ta ce an daga liyafar ne sakamakon halartar zaman makoki da jarumi Ali Nuhu ya yi a Jos, dalilin rasuwar furodusan kamfaninsa Ibrahim B. Nuhu.
A ranar juma’ar dai bangaren amarya suka shirya liyafa a Arts and Craft daura da hotel din Sheraton da ke Abuja. An ci an sha an kuma rakashe a wurin liyafar.
Wannan shi ne karo na hudu da jarumin ya yi aure, inda na farko ya auri Amina, sai A’isha, sai Maryam, sai kuma yanzu Maryam A. B Yola, a halin yanzu dai Maryam A B Yola da A’isha ne matan jarumin.
A cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai Ali Nuhu da Lawan Ahmed da Yakubu Mohammed da Tijjani Asase da Uzee da Abdul’Aziz dan Small da Umar M Sheriff da sauransu.

Share