✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da bukukuwan shekara a Kudancin Kaduna

Bukukuwan da kabilun Moro’a (Marwa) da Gworok (Kagoro) ke gudanarwa a watan farko na kowace shekara sun kasance mafiya girma a bukukuwan gargajiya da sauran…

Bukukuwan da kabilun Moro’a (Marwa) da Gworok (Kagoro) ke gudanarwa a watan farko na kowace shekara sun kasance mafiya girma a bukukuwan gargajiya da sauran kabilun ke gudanarwa a kowace shekara.

Bikin yana daga cikin dadaddun bukukuwan da ake gudanarwa a Kagoro. Asalin bikin, kamar yadda suke kiransa da suna Afan, da ke nufin tsauni ko dutse, yana da nasaba ne da fitaccen dutsen nan na Kagoro.

Kamar yadda tarihi ya nuna, bayan sun yi girbi, sai su shirya bikin farauta ta yadda suke zuwa su hau saman dutsen, domin a cewarsu, shi ne ke kare su daga harin abokan gaba.

Bikin ya ci gaba da gudana har zuwa lokacin marigayi Sarkin Kagoro Malam Gwamna Awan, wanda ya rasu a shekarar 2008 yana da shekara 93 a duniya, kuma ya yi sarauta na tsawon shekara 63 (1945-2008), wanda shi ne ya sa aka hade bikin girbin da na sabuwar shekara inda tun daga nan abin ya ci gaba da bunkasa yana daukar sabon salo.

A kan fara bikin ne da karbar fareti wanda ’yan Kungiyar Boys Brigade ke yi, suna tafe suna buga badujala sannan sauran kungiyoyin makada da maharba da ’yan rawar gargajiya kowane zai wuce sannan Gwamna ko wakilinsa zai mike don karbar faretin.

Bayan kammala wannan kashin, sai a zauna don gabatar da jawabai tare da sake gabatar da ’yan rawar gargajiya kowane ya zo ya nuna irin tasa al’adar.

A jawabin Babban Bako Mai jawabi, Shugaban Asusun Ilimin Manyan Makarantu (TETfund) Farfesa Suleiman Bogoro wanda Farfesa Andrew Haruna ya wakilta ya karfafa wa mutanen Kagoro gwiwa ne kan yin amanna da damarmakin da Najeriya ke da su don tabbatar da mafarkinta na samun ci gaba. Ya shawarci mahukunta a kasar nan su rika gudanar da adalci cikin dukkan lamuransu.

A jawabin Sarkin Kagoro Mista Ufuwai Bonet fara yaba wa dukkan bangarorin da ke bayar da goyon baya wajen dorewar wannan biki da aka kwashe shekara da shekaru ana gudanarwa ya yi. Sarkin, ya shawarci gwamnati ta rika kafa dokokin da za su amfani rayuwar talaka, inda ya yaba wa gwamnatin kan kokarinta na dakile hare-hare da tabbatar da tsaro a yankin.

Sannan ya yi kira ga al’umma su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninsu su rungumi zaman lafiya.

A jawabin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i wanda Babban Mai ba shi Shawara kan Harkokin Siyasa, Mista Ben Kure ya wakilta kira ya yi ga mutanen Kagoro su kiyayi duk wani abu da ka iya haifar da cikas wajen ci gaban kasa. Ya ce sabuwar shekarar da ake ciki wata sabuwar dama ce don aiwatar da sababbin abubuwan ci gaba ta hanyar rungumar juna da zaman lafiya tare da mara wa gwamnati baya don samun nasara.

A daya bangaren kuma, a cikin sakonsa a wajen bikin Moro’a (Marwa) Gwamnan Jihar ta bakin Shugaban Karamar Hukumar  Kaura, Dokta Bege Katuka Ayuba yaba wa al’ummar Masarautar Moro’a ya yi game da zaman lafiyar da suka samar a yankinsu, bisa la’akari da rashin zaman lafiyar da ya addabi yankinsu a shekarun baya.

Kabilar Marwa sukan shirya nasu bikin gargajiya na shekara-shekara a garin Manchok, inda akan taru domin sauraron jawabai da gabatar da wasannin kade-kade da raye-raye na gargajiya.

Shi ma kamar na Kagoro, akan fara shi ne da yin maci sai gabatar da makadan gargajiya da masu wasanni sannan sauraron jawabai tare da nishadantarwa.

A sakonsa, Sarkin Marwa, Malam Tagwai Sambo, wanda ya cika shekara 82 a duniya sannan ya shekara 52 a sarauta, ya nuna godiya ne kan zaman lafiyar da aka samu, inda ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta duba yiwuwar gyaran hanyar Kagoro zuwa Manchok zuwa Jankasa saboda lalacewarta da kuma kammala Sakandaren Kimiyya ta ’Yan mata da ke garin Manchok.

A kan kare dukkan bukukuwan Kagoro da Marwa ne ta hanyar buga wasannin sada zumunta na kwallon kafa da yamma.