✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da Maukibin bana a Kano

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya darikar kadiriyya suka gudanar da taron Maukibi karo na 66 a birnin Kano. Taron Maukibi ko kadiriyya…

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya darikar kadiriyya suka gudanar da taron Maukibi karo na 66 a birnin Kano.

Taron Maukibi ko kadiriyya biki ne mai dadadden tarihi da ake yin sa duk shekara don tunawa da ranar haihuwar Sheikh Abdulkadir Jilani wanda shi ne ya assasa darikar kadiriyya ta mabiya sufaye.

Jagororin gudanar da bikin Maukibin su ne iyalan Gidan kadiriyya, wato iyalan marigayi Sheikh Nasiru Kabara, wanda kafin rasuwarsa shi ne Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka gaba daya. A yanzu haka kuma babban dan marigayin Sheikh karibullah Nasiru Kabara ne shugaban wannan darika ta kadiriyya, a yankin.

Tun ana saura kwanaki biyu a gudanar da bikin, mabiya darikar kadiriyya daga kasashe da dama misali daga Pakistan da Libya sukan isa birnin Kano, baya ga wadanda ke cikin birane da kauyukan kasar nan, lamarin da ke sa garin Kano cikar kwari a duk lokaci irin wannan. Mutane da dama musamman masu abin hannunsu sukan yi girke-girken abinci da samar da ruwan sha inda ake tafiya da shi wurin taron Maukibin don raba wa jama’a su samu abin sawa a bakin salati.

Kuma kamar yadda aka saba mabiya darikar kadiriyya da yara daliban makarantun Islamiyya kan yi fitar dango zuwa filin Wali Maigiginya da ke titin Katsina. Da farko mabiya darikar kan taru a kofar Gidan kadiriyya sannan su bi taTitin Unguwar Makwarari su bi ta gefen Kasuwar Kurmi da Unguwar ’Yan mota da Unguwar koki zuwa filin Wali Maigiginya inda suke yada zango don gudanar da addu’o’i da jawabai. Idan yamma kuma ta yi sai jama’ar su kama hanyar dawowa cikin gari inda suke daukar hanyar Unguwar Dala zuwa Jakara, daga nan su ratso ta Unguwar Kwanar Goda zuwa Mandawari, su dire a Gidan kadiriyya da ke Unguwar Kabara.

A yayin wannan tafiya mabiya darikar da ’yan makarantun Islamiyya kan rika rera wakokin yabon Annabi (SAW) da kasidojin darikar cikin annashuwa.

Ba wannan kadai ba, mutane da dama kan yi amfani da wannan dama wajen sadar da zumunci a tsakanin junansu. Kuma ’yan kasuwa kan baje kolin hajjojinsu a zagayen Gidan kadiriyya da sassan birnin.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar wanda ya wakilci Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje a wurin taron, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano a shirye take ta yi tafiya da dukan kungiyoyin addini daban-daban da ke fadin jihar domin ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Ya ce saboda yadda aka san Gidan kadiriyya da jajircewa wajen wayar wa jama’a kai shi ya sa gwamnatin jihar ta dauki shugabancin Majalisar Shura ta Jihar ta damka shi a hannun Khalifa karibullah Nasiru Kabara.

Sai ya yi kira ga kungiyoyin addini su yi kokarin bayar da ilimi ga al’ummar jihar wanda hakan zai matukar tasiri wajen samun nagartaciiyar al’umma mai tarbiyya.

A jawabin Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka, Sheikh kariballah Nasiru Kabara ya yi kira ga malaman addinin Musulunci na kasar nan su hada kai da juna domin daukaka addinin.

Duk da karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan, mabiya darikar kadiriyya sun fito don halartar taron Maukibin tare da gudanar da dukan abubuwan da aka saba kamar yadda wani Bashir Aminu wanda ya halarci Maukibin ya shaida wa Aminiya. “Zan iya cewa armashin da Maukibin bana ya yi ya fi na shekarun baya, lura da dimbin mutanen da suka halarci Maukibin, duk da karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan,” inji shi.

Maukibin na bana ya samu tagomashi, inda jami’an tsaro suka kawar da kai ga masu babura suka rika daukar fasinjoji, duk da cewa akwai da dokar da ta hana daukar fasinja a kan babura, wadda ta samo asali lokacin da ’yan Boko Haram suka rika kai hare-hare a jihar.

Haka kuma kasancewar Maukibin ya fado a ranar Asabar din karshen wata da gwamnatin jihar ta ware don gudanar da tsabtar muhalli daga karfe 7 zuwa 10 na safe, a wannan rana ta Maukibin, gwamnatin ta janye dokar domin masu Maukibin su samu fita su gudanar da shi.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron sun hada da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano da Wamban Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da manyan ’yan kasuwan jihar da suka hada da Alhaji Salisu Sambajo da Alhaji Sabi’u Bako da sauransu.