✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kai wa jiragen dakon man fetur din Saudiyya hari a iyakar tekun Fasha

An kai hari kan jiragen dakon man fetur biyu na Saudiyya a kusa da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar Ministan Makamashi  na Saudiyyar Khalid…

An kai hari kan jiragen dakon man fetur biyu na Saudiyya a kusa da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar Ministan Makamashi  na Saudiyyar Khalid al-Falih.

Lamarin, wanda ya faru kusa da tashar jirgin ruwa ta birnin Fujairah da ke mashigar Gulf a wajen mashigar teku ta ‘’Strait of Hormuz’’ ya hallaka wasu daga cikin wadanda suke cikin jiragen ruwan a cewar Khalid al-Falih.

Iran, wacce ta hada iyaka da mashigar, ta ce lamarin abin damuwa ne da kuma tausayi kuma ta yi kira da a gudanar da bincike.

Yankin da ke samar da akalla kashi daya cikin biyar na man da ake samar wa duk duniya, na ci gaba da fama da rashin kwanciyar hankali.

Amurka dai ta aika jiragen yaki a cikin ’yan kwanakin nan domin tunkarar abin da ta kira alamun barazana daga Iran zuwa ga dakarunta da kuma sauran jami’an ruwa da ke aiki a yankin.

Iran dai ta yi watsi da dukkanin zarge-zargen a inda ta ce ba wata hujja.

A cikin watan da ya gabata, Iran ta yi gargadin rufe mashigar tekunta ta Strait of Hormuz  idan an hana ta amfani da hanyar ta ruwa bayan da Amurka ta yanke wani hukunci na cire tankunkumi kan manyan ’yan Iran masu sayan man fetur.

Har yanzu dai ba a bayyana bayanai sosai kan harin ba, wanda aka ce ya faru da karfe shida na safe a kasar, cikin tekun da ke yankin UAE na mashigar Gulf ta kasar Oman, wato gabashin birnin Fujairah kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta UAE ta ce, “Jami’an UAE sun dauki dukkanin matakan da ya kamata kuma suna gudanar da bincike kan lamarin.”

A safiyar ranar Litinin, Kamfanin Dilancin Labarai na Saudiyya ya ce Mista Falih ya fada cewa akwai wasu tankunan man fetur biyu na Saudiyya da aka kai wa hari.

‘’Daya daga cikin jiragen na kan hanyarsa ta zuwa inda za a dora masa danyen man fetur na Saudiyya daga tashar jirgagen ruwa ta Ras Tanura, wanda zai kai wa abokan cinikin Kamfanin Saudi Aramco da ke Amurka,”

Bayan wannan kuma, wani kamfani mai kula da jiragen ya ce wani abin da ba a san mene ne ba ya barnata jiragen ruwan Norway a kusa da Fujairah.

‘’Masu aiki a jirgin dai ba su samu raunuka ba, duk da cewa jirgin ya huje,’’ A cewar kamfanin Thome Ship management

Ita dai Saudiyya da ma Hadaddiyar Daular Larabawa ba su zargi kowace kasa ko kungiya da harin ba.

Amma Mista Falih ya ce an kai harin ne domin takaita walwalar jiragen ruwa da kuma tsaron yadda ake rarraba kayayyakin man fetur zuwa ga sauran yankunan duniya.

Ya kuma kara da cewa kungiyoyin duniya suna na da alhakin tsare walwalar jiragen ruwa da kuma tsaron tankunan mai.