Da Dumi Dumi

Yadda aka kama masu satar yara a Kano su siyar a Anambra

Rundunar ‘yan sandan Kano a ranar Juma’a ta kubutar da yara tara da aka yi garkuwa da su a Kano aka siyar da su a jihar Anambra, yanzu haka an mika su ga iyayensu.

Ana zargin wadanda aka kama da yin garkuwa da yaran tare da siyar da su a jihar Anambra a matsayin safarar yara, wadanda shekarun su ya fara daga 2 zuwa 10, an dai sace yaran daga yankunan cikin birnin jihar lokuta daban daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmed Iliyasu, wanda ya mika yaran ga iyayen su ya ce a yanzu haka akwai wadanda suka bace tun shekarar 2014, amma an yi nasarar gano wasu daga cikin yaran da aka siyar a jihar Anambra.

A yanzu haka an kama mutum 8 da ake zargin su da sace yaran a Kano su  siyar a jihar Anambra.

ADVERTISEMENT
Share