✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kama Wadume a Kano

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan sanda suka kama gawurtaccen wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Jihar Taraba, Hamisu Bala Wadume…

A ranar Litinin da ta gabata ce ’yan sanda suka kama gawurtaccen wanda ake zargi da garkuwa da mutane a Jihar Taraba, Hamisu Bala Wadume a cikin wani kantin sayar da kayyayaki da ake kira da Mai Allo Plaza da ke Karamar Hukumar Gezawa a Jihar Kano.

Hamisu Wadume ’yan sanda ne suka fara kama shi a kwanakin baya a garin Ibi a Jihar Taraba sai dai kuma an zargi sojoji da kashe ’yan sanda uku da raunata wadansu kafin su sake shi.

Kakakin Hedkwatar ’Yan sandan Najeriya, Frank Mba a takardar da ya sanya wa hannu ya ce jami’ansu ne suka sake kama Wadume wanda ya  tsere.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru a wani faifan bidiyo bayan kama shi, wanda ake zargi Hamisu Wadume ya ce sojoji ne suka taimaka masa bayan ’yan sanda sun kama shi inda shi kuma ya tsallaka zuwa Jihar Kano “Bayan ’yan sanda sun kama ni a Ibi sai sojoji suka zo suka bude musu wuta har suka kashe wadansu daga cikin ’yan sandan. Daga nan sai sojojin suka dauke ni inda suka kai ni hedikwatarsu suka kwance min ankwa daga nan ni kuma na gudu,” inji shi.

Wani makwabcin gidan da aka kama Wadume a ciki, Malam Isa Adamu ya cewa Wadume ya shafe kwana biyar da tarewa a gidan kafin ’yan sandan su kama shi a ranar.

“Kwanansa biyar kacal a gidan duk da cewa an dade da zuba kaya a ciki, amma wannan ne karon farko da mutane suka tare a gidan domin mun ga har da mata da yara a ciki,” inji shi.

Malam Isyaku Baiku shi ne Mai unguwar Tsamiyar Kuka, unguwar da aka kama  Wadume, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce za su dauKI matakin shari’a a kan duk dillalin da yake kawo musu batagari a unguwarsu.

“Dillalai ne ke kawo mana irin wadannan matsaloli, inda suke sa haya ko sayar da gida ba tare da bincike ba. Kuma mu a matsayinmu na masu gari ba a sanar da mu idan ana kawo mutum. Ka ga wanann ai ba daidai ba ne. Don haka yanzu za mu dauki matakin shari’a akan duk wani dillali da ya kawo mana batagari a yankinmu,” inji shi.