Da Dumi Dumi

Yadda aka kama wanda ya kashe Kwamandar Sojin Ruwa a Kaduna

Kwamandar Sojin Ruwa Oluwayemisi Ogundana
Kwamandar Sojin Ruwa Oluwayemisi Ogundana

Wanda ake zargi da kashe Kwamandar Sojan Ruwa Oluwayemisi Ogundana da ke Shugabantar Sakandaren Kwalejin Horar da Manyan Hafsoshin Soji (CSC) da ke Jaji mai sana Mists Simon Bernard ya shiga  hannu.

Majiyar Aminiya ta ce dubun wanda ake zargin Mista Simon Bernard ya cika ne bayan da sojojin sama  suka kama motar marigayiyar kirar Toyota Highlander lokacin da wani direba farar hula daga Jaji ya tsaya a harabar rundunar sojojin sama domin ya kara man fetur, inda kafin ya dawo daga sayo man fetur din ’yan sanda sojojin saman Najeriya suka yi wa motar kwanton bauna da direban ya dawo  suka kama shi.

Majiyar ta kara da cewa bayan da suka kama shi ne suka tafi da shi ofishinsu don bincike kan yadda ya samu motar da inda zai tafi da ita.

Majiyar ta ce a yayin binciken ne sai direban ya bayyana cewa an ba shi motar ce ya sayar, kuma wanda ya ba shi mai suna Simon Bernard yana Jaji a Jihar Kaduna, sai suka baza komarsu a Jaji inda suka kwashe kwana uku suna tarkon Simon Bernard kafin  su kama shi.

Wanda ake zargin ya tabbatar cewa shi ne ya kashe ta bisa wasu matsaloli da ke tsakaninsu, kamar cire shi da ta sa aka yi daga matsayin Shugaban Kungiyar Malamai (PTA) na makarantar da take shugabanta, da kuma kin cika masa alkawarin kudi da ta yi na Naira miliyan biyu da rabi, wanda hakan ya sa ya kashe ta, ya daddatsa gawarta ya jefa a cikin rijiya a  kauyen Unguwar Lauya da ke bayan Barikin Jaji.

ADVERTISEMENT

Da Aminiya ta ziyarci garin Jaji ta samu jama’ar garin na ta sharhi kan irin yadda lamarin ya faru, tare da bayyana cewa marigayiyar ta yarda da shi wanda ake zargin, duk da jama’a suna tsoron furta wani abu kan lamarin.

Aminiya ta yi kokorin kaiwa kauyen Unguwar Lauya da ke hade da barikin sojoji na Jaji inda lamarin ya faru amma abin ya ci tura saboda ko su mutanen unguwar sai sun nuna katin izini shiga kafin a bar su wuce zuwa gidajensu.

Share