✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka karrama Ali Nuhu a Indiya

A makon jiya ne aka karrama jarumi kuma darakta a Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarki a kasar Indiya. Wadansu dalibai…

A makon jiya ne aka karrama jarumi kuma darakta a Masana’antar Kannywood, Ali Nuhu wanda aka fi sani da Sarki a kasar Indiya.

Wadansu dalibai ’yan Arewacin Najeriya da ke karatu a kasar Indiya da malamansu Indiyawa ne suka gayyaci jarumin bikin Ranar Al’adu kuma suka karrama shi a wajen taron.

“Daliban na karanta fannoni daban-daban kama daga fannin likita zuwa hada magunguna da injiniya da sauransu,” in ji Ali Nuhu kamar yadda ya shaida wa BBC. Jarumin ya ce baya ga wadannan dalibai, wasu makarantu a kasar sun ba shi lambobin yabo.

Ali Nuhu ya ce “Akwai makarantar Dayananda Sagar School of Physiotherapy su ma sun ba ni lambar yabo kuma sun nuna jin dadinsu kan yadda daliban Najeriya ke mayar da hankali kan karatunsu.”

Jarumin ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa da kuma yadda malaman wadannan makarantu ke da sha’awar al’adun Hausawa. “Wadansu daga cikin malaman har fina-finan Hausa suke kallo saboda su ga yadda yanayin rayuwar Bahaushe take.

“Shi ya sa idan wani dan wasa ya zo taro irin wannan sukan karrama shi,” inji Ali Nuhu.