✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe Mataimakiyar Darakta ta fadar shugaban kasa

Sabbin bayanai sun nuna yadda aka kashe Mataimakiyar Darakta a fadar shugaban kasa ta Aso rock, Abuja. Matar mai suna Laetitia Naankang Dagan, tana aiki…

Sabbin bayanai sun nuna yadda aka kashe Mataimakiyar Darakta a fadar shugaban kasa ta Aso rock, Abuja. Matar mai suna Laetitia Naankang Dagan, tana aiki ne a matsayin Mataimakiyar Darakta a bangaren kulawa da walwala a fadar shugaban kasar Najeriya.

Marigayiyar tana rayuwa ne a wani gida da ke rukunin gidaje na EFAB, Lokogoma, Abuja. Wakilan Aminiya sun gano cewa, wadanda suka kashe matar sai da suka daure ta, suka yi lalata da ita kafin su bankawa gadonta wuta suka tsere a daren ranar Litinin.

Wakilan da suka ziyarci gidan da abin ya faru sun samu gidan a kulle sa’anan makwabtan gidan, inda suka same su cikin firgici suka yin bayani.

Masu tsaron rukunin gidajen sun bayyana cewa, sun hango hayaki na fitowa daga gidan lokacin da sukaje gidan saboda kai agajin gaggawa. Daya daga cikin masu tsaron wanda bai so a ambaci sunansa bai bayyana cewa, ‘yar uwar matar da ke zaune a anguwar Lugbe, Abuja ce ta kira su taba su bayanin cewa marigayiyar na cikin hadari.

Ya kara da cewa, ‘yar uwar marigayiyar ta shaida musu cewa ta kira marigayiyar da karfe 10:30 na dare inda marigayiyar take kuwwar cewa wasu na shirin kasheta wanda daga baya wayarta ta daina shiga.

“Mun isa gidan wajen karfe 12:00 na dare muka samu kofar gidan a kulle sai muka yanke shawarar tsallakawa ta Katanga. Da muka shiga mun hango hayaki na fitowa daga dakinta amma muka yi kokari muka shiga dakin. A nan ne muka tarar da marigayiyar a daure jikin gadonta tsirara.” in ji mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa.

Aminiya ta kuma gano cewa, akwai wasu samari da ke rayuwa tare da marigayiyar a gidan kuma tuni sun tsere. Tuni dai an damke daya daga cikinsu wanda aka kama da waya hannu ta marigayiyar inda ya canja hotonta na manhajar WhatsApp zuwa nashi.

Da aka tuntube shi, mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja DSP Anjuguri Manzah, ya tabbatar da damke wanda ake zargin mai suna Edirin Ohonre.

Anjuguri Manzah, ya bayyana cewa ‘yan sanda sun baza komar su saboda tabbatar da cewa, an kama duk wanda ke da hannu a cikin kisan.

Ya kara da cewa, wanda aka kama din yana bada bayanai masu muhimmanci da zasu taimaka wajen kamo sauran wadanda ke da hannu cikin al’amarin.