Da Dumi Dumi

Yadda aka kubutar da Magajin Garin Daura

Yadda ‘yan sanda suka ceto Magajin Garin Daura
Yadda ‘yan sanda suka ceto Magajin Garin Daura

A ranar Talatar da ta gabata ce Rundunar ’Yan sandan Najeriya a karkashin jagorancin sashin musamman na Yaki da Miyagun Laifuffuka na Ofishin Sufeto Janar da ke karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari da hadin gwiwar Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano suka yi nasarar kubutar da Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba daga hannun masu garkuwa da shi bayan ya shafe wata biyu a tsare.

Idan za a iya tunawa, tun a ranar daya ga watan Mayu da ya gabata ne wadansu ’yan bindiga suka sace Magajin Garin Daura a gidansa da ke garin Daura a Jihar Katsina.

Da yake yi wa manema labarai karin haske, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an gudanar da shirin ceto Magajin Garin Dauran ne da kimanin karfe 2:00 na dare, inda aka yi nasarar kubutar da shi ba tare da rauni ba.

A cewar DSP Haruna, jami’an tsaro sun kama wadansu daga cikin masu garkuwar sannan sun gano makamai a gidan. “Ba zan iya fadin yawan mutanen da aka kama ba, kasancewar an gudanar da aikin ne a karkashin jagorancin ayarin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya,” inji shi.

Ku nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.

ADVERTISEMENT

Share