✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace jaririn kurma jim kadan da haihuwarsa

A ranar Larabar makon jiya ne wani abin tausayi ya faru a asibitin Yusuf dantsoho da ke Tudun Wada Kaduna inda aka sace jaririn wata…

A ranar Larabar makon jiya ne wani abin tausayi ya faru a asibitin Yusuf dantsoho da ke Tudun Wada Kaduna inda aka sace jaririn wata kurma jim kadan da haihuwarsa.

Maihaifiyar jaririn mai suna Salamatu Kabiru da mahaifinsa Kabiru dukansu kurame ne, kuma sai da aka yi mata aiki kafin ta haihu a ranar kuma tana kwance tana bai wa jiririn nono ne wata mace ta shigo dakin ta karbi dan daga hannunta.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9:00 na dare bayan mahaifin jaririn Kabiru ya fadi a kasa cikin kaduwa sakamakon ba shi wata takarda domin ya je ya sayo wani magani da za a bai wa matarsa.

A cewar wadansu da suke asibitin lokacin da lamarin ya auku sun ce sun ga matar da ta sace jaririn tana ta yawo a cikin mata ’yan rakiya a bakin dakin haihuwa na asibitin kafin haihuwar. 

Aminiya ta gana da Salamatu Kabiru a lokacin da suka je ofishin Kwamishinar Mata da Jin Dadin Nakassasu Hajiya Hafsat Baba.

A cewarta, ta bakin wani tafinta lokacin da matar ta karbi jaririn daga hannunta tana fama da kasala saboda aikin da aka yi mata. Ta ce a tunaninta matar taimakonta za ta yi ta ajIye jaririn a gadon da ke gefenta domin a lokacin hankalin ’yan uwanta ya koma wajen mijinta Kabiru wanda ya fadi a kasa.

A cikin wannan rudani ne matar ta lullube jaririn cikin zane ta fice daga dakin ba tare da an ganta ba.

kokarin jin ta bakin mijin ya ci tura domin baya nan lokacin da Aminiya ta ziyarci ofishin Kwamishinar sai dai kanwar mahaifinsa wanda ta ce kamar uwa take gare shi mai suna Amina Yahaya, inda ta ce hankalinsu ya tashi ne a lokacin da Kabiru ya fadi.

“Da muka je muna ta kokarin tayar da shi (Kabiru) ashe ita matar ta karbi jaririn daga hannun Salamatu lokacin da take shayar da shi ta fice daga dakin ba mu sani ba,” inji ta.

Ta ce hakika lamarin ya tayar musu da hankali matuka domin babu matar da za ta so ta rabu da jaririnta ’yan sa’o’i kadan da haihuwarsa.

Shugaban Asibitin Yusuf dantsoho, Dokta Muhammed Bello Armaya’u ya nuna alhininsa game da abin da ya faru inda ya ce tuni an sanar da ’yan sanda domin yin bincike a kan lamarin.

Ya ce matar da ake zargi da satar jaririn ta dade a cikin matan da suka yi rakiya zuwa asibiti wanda hakan ya sa ake ganin tare suke da ita.

“Babu sakacin hukumar asibitin, amma za mu dauki matakan ganin hakan bai sake faruwa ba. ýDomin matar da ake zargi ta zauna da su kusan sa’o’i takwas kuma su ba su ce ba ’yar uwarsu ba ce balle a kore ta. Dole mu tausaya musu, duk da mu maza ne ba haihuwa muke yi ba, amma mun san dadin ’ya’ya, shi ya sa muke cewa a ci gaba da yin addu’a Allah Ya sa a gano matar,” inji shi. 

Ya kara da cewa: “Matar an ce ta shigo da wani yaronta dan kimanin shekara 12 domin bayan ta karbi jaririn ta yi kamar za ta ajiye mata a kan gado amma sai ta fice. Ba mu zargin kowa domin abin ya ba mu mamaki muna kuma ba da hakuri idan har mun yi kuskure. Kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya na yanzu dan uwan wanda aka sace wa jaririn ne wanda hakan ke nuna maka ba mu da wani abin boyewa dangane da lamarin. Wannan ne farko da aka taba samun irin haka ya faru domin kowa ya san asibitin Dutse babu dakin haihuwa da ya fi namu inganci da kulawa,” inji shi.

kungiyar Nakassasu ta Jihar Kaduna ta nemi gwamnatin jihar ta sa baki wajen ganin an gano jaririn da aka sace. A cikin wata wasika dauke da hannun Sulaiman Abdul’azeezý wadda aka mika wa Kwamishinar Mata da Jin Dadin Nakasassu, Hafsat Baba sun bukaci a nemo matar da ta aikata laifin.

Ita ma Kwamishina Hafsat Baba a jawabinta ta nuna damuwa inda ta ce za su hada hannu da Ma’aikatar Lafiya wajen gudanar da binciken domin sanin gaskiyar abin da ya faru.

A cewarta, Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i ba zai ji dadin abin da ya faru ba don haka sai ta tabbatar wa iyayen jaririn da ’ya’yan kungiyar Nakassasu ta Jihar cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace wajen gano wannan mata domin hukunta ta.