✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda aka sayar da mu a matsayin bayi a kasar Libya’

Aminiya ta zanta da wani matashi mai suna Muhammad Sani Abdullahi  da ya kasance daya daga cikin matasan da wani mutum ya dauke su zuwa…

Aminiya ta zanta da wani matashi mai suna Muhammad Sani Abdullahi  da ya kasance daya daga cikin matasan da wani mutum ya dauke su zuwa kasar Libya bisa alkawarin zai samar musu aiki mai tsoka, amma maimakon haka aka sayar da su a matsayin bayi:

 

An ce an sayar da ku a matsayi bayi a Libya, yaya abin da ya faru?

Mun tafi Libya ne mu hudu, wato ni Muhammad Sani Abdullahi da Umar Abubakar da Bashir Abdullahi da Musa Muhammad. Wani bawan Allah a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna ya kwadaita mana cewa zai sama mana aiki mai tsoka. Ya ce idan a nan gida Najeriya mutum yana samun Naira dubu 10 a kowace rana, a can a kullum mutum zai samu Naira dubu 20, ko dubu 25. Ya ce akwai aikin zaman shago da aikin kanikanci da aikin tuka mota da sauransu.  Ya ce amma za mu ba shi Naira dubu 40 kowannemu kuma zai kai mu har Agadas da ke kasar Nijar. Idan muka je Agadas daga can zai sanya mu a mota zuwa Libya.  Kuma idan mun fara aiki za mu biya Dinari dubu hudu kudin kasar Libya, kusan Naira miliyan 1 ke nan.

Muka tashi daga Kano muka isa Agadas, sai aka dauke mu a mota zuwa Libya, mun kai mota sama da 50 kowace dauke da mutane, wadansu mutum 20 wadansu mutum 25. Mun tashi ranar 15 ga watan Yuni, muka isa Birnin Sabha na kasar Libya a ranar 20 ga watan Yunin. Muna isa aka boye mu, domin idan aka ga bakaken fata ’yan ci-rani za a kama su. Haka za ka ga ana ta guje-guje da ku a bayan gari. Har a samu wani gida a boye ku.

Tunda muka isa kasar kullum sai yaudara, gobe za a kai mu wajen aiki, haka aka yi ta yaudararmu. Mu kuma muna ta tunanin gida mun bar iyalanmu, muna kulle babu fita balle zuwa yawo, muna jin kiran Sallah babu dama mu fita mu yi Sallah, har tsawon wata uku muna jira.

Shi ne sai  matar da aka hada mu da ita ta  hada baki da wani Balarabe, kan cewa a zo a sayar da mu. Domin a kasar Libya ana sayar da mutane kamar yadda za ka kama ragonka, ka kai kasuwa ka sayar a nan gida Najeriya. Don haka wannan mata ta sayar da mu, har an kira mai sayen ya zo da mota zai dauke mu, muka samu Allah Ya ba mu sa’a muka tsere.

Sai muka samu wani bawan Allah mutumin kasar Nijar, amma ya dade a kasar Libya. Shi ne muka yi magana da shi muka ce muna son ya taimake mu ya hada mu da wani wakilin jama’a na Najeriya. Shi ne ya kwatanta mana wajen da za mu je. Da muka isa wajen muka yi tambaya aka hada mu da wani bawan Allah mai suna Malam Aminu Tela.  Asalinsa mutumin Zariya ne, shi ne muka zauna da shi muka yi masa bayanin halin da muke ciki.  Shi ne ya kai mu gidansa.

Bayan mun gudu daga gidan da aka tsare mu, zuwa gidan wannan mutum da ya taimake mu,  mun samu labarin cewa hankali ya tashi kan rashin ganinmu a gidan da aka tsare mu, saboda kada mu je mu tona asirin abin da suka yi mana.

Bayan mun yi kwana bakwai, sai na fita na kewaya ko zan ji wani labari sai na hadu da wani mutumin da yake kula da wannan gida da aka tsare mu. Ya ce mini an ce da an gan ni a kama ni, domin an riga an sayar da ni. Da na ji wannan labari shi ne na canja hanya na koma gida.

Tunda na koma ban kara fitowa  ba, sai da na yi kwaa 14, shi ne wannan mutum ya dauke mu ya biya mana fasfo ya yi mana biza. Muka samu aka hada mu da mutanen da za a kwaso zuwa Najeriya, aka tausaya mana saboda ganin halin da muke ciki, har an gama hada mutanen da za a kwasa, amma Ofishin Jakadancin Najeriya suka taimaka mana aka sako mu a jirgi a ranar alhamis 4 ga Oktioba daga birnin Sabha zuwa Najeriya.

Babu shakka sun kula da mu sosai sun ba mu abinci da tsaro, bayan da muka sauka a gida Najeriya a filin saukar jiragen sama na Legas. Jami’an shige-da-fice suka duba mu, bayan da suka gama aka ba mu wurin kwana, a ranar Juma’a suka ba mu kudin mota, muka shigo mota zuwa gida.

Idan aka sayar da mutum a matsayin bawa,  yaya suke yi da shi?

Wanda ya saya zai tafi da mutumin ya ya daure shi, mutum ya zama bawa ke nan.  Akwai wani waje da ake kira Mazara, akalla tafiyar kilomita dubu biyu daga Sabha. Idan aka kai mutum ko an ce ya tafi ba zai iya ba, saboda ya riga ya jigata. Kuma idan an kai mutum, kullum zai fara aiki tunda safe har zuwa karfe 6 na yamma. Kuma ayyukan da suke sanya mutane suna yi akwai aikin lambu da aikin kiwon rakuma da awaki da dawaki da kaji da sauransu. Duk za ka yi wadannan ayyuka  a matsayin bawa.  Haka mutum zai yi ta zama a wannan waje, daga nan idan wanda ya saye shi ya gaji da shi, sai ya dauke shi ya sayar wa wani.

A matsayinka na wanda ya gane wa idonsa halin da masu zuwa neman kudi suke ciki a kasar Libya, yaya ka ga halin da ’yan Najeriya suke ciki a wancan kasa?

A gaskiya su mutanen Libya a wajensu bakake ba komai suke ba, kare ma ya fi su daraja. Don haka ina jawo hankalin ’yan Najeriya kowa ya zauna inda Allah Ya ajiye shi domin kasarsa ta fi kowace kasa a duniya. Idan mutum zai fita ya samu Naira 100 ko Naira 200 ko zai fita bai samu komai ba, gobe in ya fita Allah zai ba shi.

A  Najeriya muna da jihohi 36 ko’ina mutum ya je a wadannan jihohi zai samu abin da zai yi. Ya fi mutum ya haura ya bar kasar nan, ya tafi wata kasa. Wallahi mutane suna wulakanta sosai a kasar Libya. Balaraben Libya zai iya daukar ka ka yi masa aiki, bayan ka gama ya ce ba zai biya ba, idan ka yi masa taurin kai ya dauko bindiga ya ce zai harbe ka.