✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka taimaka wa mesa ta hadeye akuyar manomi

Mutanen wani kauye a China sun taimaka wa wata mesa da ke hadiye awakin wani manomi. Mesa mai tsawon mita hudu tana hadiye awakin ne…

Mutanen wani kauye a China sun taimaka wa wata mesa da ke hadiye awakin wani manomi. Mesa mai tsawon mita hudu tana hadiye awakin ne ba a sani ba kafin a gano haka a kusa da gidan gonar mutumin a  Karamar Hukumar Andi a Lardin Fujian a kasar China.

Mazauna kauyen Kuanzhou, a Lardin Fujian da ke Kudu maso Gabashin China, sun ce mesar ta kai kusan awa daya tana amayar  da dabbobin da ta hadiye sai da ya kai  wani ya matse jellar macijiyar, saboda hadiyar da take yi kamar za ta mutu.

Makiyayin mai suna Mista Yao, ya ce daga farkon bana ya rasa awaki sama 20, kuma ya gano akuyarsa da ta bace a saman tsauni macijiyar na yunkurin hadiyarta.

“Cikin wannan mesa ya kumbura, na tabbatar da wannan ita ce take cinye min awaki idan suka bace,” inji shi.

Mista Yao, ya bukaci ’yan sandan daji da sauran jama’ar kauyen su taimaka masa game da bacewar awakinsa. Hakan ya sa aka taru aka rika tura jelar mesar ta yadda za ta samu saukin hadiyar akuyar.

“An kai kusan sa’a daya don kawai macijiyar ta kammala hadiye akuyar,” inji shi.

An gano macijiyar tana hadiyar akuyar ce ta alamar kafar akuyar bayan ta hadiye sauran jikin da kan akuyar mai nauyin kilo 40.

Daga bisani dai ’yan sandan da ke lura da dajin sun tafi da mesar gidan adana dabbobi na ‘Andi Temporary Wild Animal Shelter.’

Nan gaba za a kyale mesar don ci gaba da rayuwa, saboda jinsin macijiya na cikin dabbobin da ake adanawa a kasar China.