✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a ofishin CBN

Rahotannin sun kara fitowa kan zanga-zangar #EndSARS a Abuja , inda daga baya-bayan nan masu zanga-zangar suka yi zaman dirshen a daura da Babban Bankin…

Rahotannin sun kara fitowa kan zanga-zangar #EndSARS a Abuja , inda daga baya-bayan nan masu zanga-zangar suka yi zaman dirshen a daura da Babban Bankin Najeriya (CBN)  a Birnin.

A ranar Lahadi matasan da ke zanga-zangar sun taru a daura da CBN da ke yankin kasuwanci na Abuja, inda suka tare tituna 4 da suka ratsa ta wajen, wasu kuma suka taru a kan gadar sama da ke kusa da bankin.

Aminiya ta samu labarin cewa, tun daga misalin karfe 2 na ranar dubbban matasa suka mamaye wajen domin yin zaman dirshan tare da yunkurin hana CBN aiki a ranar Litinin.

Wani shaida ya ce masu zanga-zangar sun yi ta dukar motocin da suka ratsa ta wajen, a yayin da wasu motoci da dama su ka makale a wajen na tsawon lokaci, ba tare da samun wucewa ba.

Bayanai sun ce, da misalin karfe 3 na asubahin Litinin, wasu ‘yan farauta yawancinsu matasa su kusan 500 suka kai samame wajen tare da auka wa masu zanga-zangar.

Wata majiya mai kusanci da ‘yan farautar da ta kira “Kungiyar Samar da Zaman Lafiya”, ta ce matasan sun yi ta kai kora a tsakaninsu da masu zanga-zangar wadanda a karseh suka cika  bujensu da iska su tsere.

Ta ce an banka wa motoci biyu na ‘yan zanga-zangar da a ka bari a wajen, wuta.

Sai dai majiyar ta ki ba da bahasi a kan ko akwai wadanda aka raunata daga bangaren abokan masu zanga-zangar ko rashin rai.

Ta ce “Ba wutan lantarki a lokacin, a saboda haka ba zan iya sanin ko akwai hakan ba”, inji shaidar.