✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka tuna da Thomas Sankara a Burkina Faso

Yayin da aka cika shekara 31 da kisan gillar da aka yi wa Shugaban Burkina Faso Kyaftin Thomas Sankara, masoyansa a kasar musamman magoya bayan…

Yayin da aka cika shekara 31 da kisan gillar da aka yi wa Shugaban Burkina Faso Kyaftin Thomas Sankara, masoyansa a kasar musamman magoya bayan Jam’iyyar MPN, sun shirya wani biki domin tunawa da kyawawan dabi’un mamacin, da ake yi wa kallon wani gwarzo mai akidar kare martabar Afirka a idon duniya.

Muryar Amurka ta sanya muryar marigayi Thomas Sankara a wani lokacin taron shugabannin kasashen Afirka, inda yake jan hankalinsu a kan illar bashin da kasashe masu tasowa ke ciyowa daga bankin duniya da asusun bayar da lamani (IMF).

“Gamsuwa da yadda Thomas Sankara ya dage da ayyukan mai do da martabar Afirka ya sa a yau ake begensa,” inji Farfesa Boube Na Maiwa malami a Jami’ar Sheik Eeik Anta Diop ta Dakar Senegal.

Jam’iyyar MPN wace aka kafa a karkashin turba irin ta yaki da miyagun halayen shugabanni, na daukar Thomas Sankara a matsayin wani gwarzon da matasan yau za su dauki darussa daga tsarin rayuwarsa, wanda hakan ya sa suka shirya taron muhawara da tattaunawa a kan tarihin marigayin.

Shekara 31 bayan rasuwar Thomas Sankara, iyalinsa da sauran makusantansa na jiran ganin hukumomin Burkina Faso sun zakulo wadanda suka hallaka shi sai dai har yanzu shiru babu labari.

A ranar 15 ga Oktoban 1987 ne wadansu sojoji a karksahin jagorancin Kyaftin Balise Compaore suka yi wa Kyaftin Thomas Sankara kisan gilla a lokacin da suke kokarin kifar da gwamnatinsa daga karagar mulkin kasar bayan ya shafe shekara kusan 4 a kan mulkin. Juyin mulkin da ake hasashen an tsara shi da nufin murkushe fito-na-fito da marigayin ya kaddamar da Turawa saboda zarginsu da cin hakkokin Afirka da ‘ya’yanta.