✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi bikin rantsar da shugabannin MOPPAN a Minna

kungiyar Masu Shirya Fina-Finai Ta Najeriya (MOPPAN), reshen Jihar ta gudanar da bikin rantsar da sabbabin shugabanninta.An gudanar da bikin rantsar da shugabannin da suka…

Sababbin shugabannin kungiyar MOPPAN na Jihar Neja ake rantsarwa kungiyar Masu Shirya Fina-Finai Ta Najeriya (MOPPAN), reshen Jihar ta gudanar da bikin rantsar da sabbabin shugabanninta.
An gudanar da bikin rantsar da shugabannin da suka hada da na ‘yan wasa da na mawaka da kuma na marubutan ne a Cibiyar Raya Al’adun Gargajiya ta U.K Bello inda jama’a daga sassa daban-daban a ciki da wajen Jihar suka halarta domin nuna goyon bayansu.
Da yake jawabi, Shugaban kungiyar reshen Jihar Neja, Malam Muhammad Abdullahi Babagana ya yi waiwaye ne game da irin gwagwarmayar da suka yi shekara fiye da 10, kafin su samu nasarorin da suke alfahari da su.
Ya ce, “A  wadannan shekarun mun samar da fina-finan manyan harsunan Jihar nan da suka hada da na Nufanci da Gwaranci wadanda ake samu a duk fadin kasar nan.”
Ya ce, kungiyarsu tana da kyakkyawar alaka tsakaninta da takwarorinta na shiyyoyin Arewaci da na Kudancin kasar nan, domin sun yi wasanni da wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan da suka hada da su Ali Nuhu da Adam Zango da Jamila Umar da Zainab Abdullahi (Indomie).
Shugaban  ya bayyana babban kalubalen da suke fama da su sun sun hada da rashin samun cikakken hadin kai daga wurin jama’a na taimaka musu da kayan aikin da za su yi amfani da su a lokutan da bukatar hakan ta taso, wanda ba ya rasa nasaba da rashin wuraren shirya fina-finansu.
A mukalar da ya gabatar, Malami a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai, Mista Ibrahim Daniel, ya bayyana muhimmiyar rawar da masana’antar fina-finai ta taka wurin bunkasa tattalin arzikin wannan kasar da ta dogara ga albarkatun man fetur, inda ya kawo misali da kasashen Indiya da Amurka da Ingila inda fannin ke samar wa tattalin arzikinsu dubban miliyoyin daloli ga Gwamnatocinsu.
Ya ce, akwai bukatar Gwamnatocin Tarayya da na Jihohi da ma matakan kananan hukumomi su rika amfani da masana’antar fim don isar da sakonninsu.
Mai ba Gwamnan Jihar Neja Shawara kan Al’amuran Addini, Sheikh Shariff Adam El-Yakub, ya nuna takaicinsa ganin yadda al’umma ta yi wa fannin mummunar fahimta ciki har da masana addini, ya ce fannin na da rawar da zai taka wurin isar da sakonnin da jama’a za su dauka cikin lokaci kankane.
Sheikh El-Yakub daya daga cikin ‘yan wasan da aka shirya wasu fina-finan da aka shirya a wannan Jihar ya ce masana’antar na bukatar gudunmuwar malaman addini muddin ana so a samu biyan bukata.
Ya nemi masu shirya fina-finai musamman na addini su rika zuwa wurin masana domin samun sahihan labaran da za su taimaka domin samun biyan bukata. Don haka, shirya irin wadannan fina-finan na bukatar zurfafa bincike da kuma bin ka’idojin addini.
Malam Bala Anka daya daga cikin fitattun masu shirya fina-finai a Jihar Neja, ya shaida wa Wakilin Aminiya cewar suna matukar taka-tsantsan kafin su ba dan wasa damar shiga harkar fim, wanda ya hada da nemo izini daga wurin iyayensa ko wadanda yake rikonsa, “ba wai muna zuwa bakin titi ne muna dauko ‘yan wasan da suke amfani da su ba.”