✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi garkuwa da ’yan canji aka hallaka su a Legas

Wadansu da ake zargi ’yan kungiyar asiri ne sun yaudari wadansu mutum biyu da ke hada-hada a Kasuwar Canjin Kudade a yankin Ikurodu, Legas, inda…

Wadansu da ake zargi ’yan kungiyar asiri ne sun yaudari wadansu mutum biyu da ke hada-hada a Kasuwar Canjin Kudade a yankin Ikurodu, Legas, inda suka yi garkuwa da su kuma suka hallaka su.

Alhaji Munkaila Musa kanen daya daga cikin ’yan kasuwar canjin da aka yi garkuwa da su, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a ranar 14 ga Maris, inda wani matashi ya zo kasuwar tasu ya ce akwai ’yar uwarsa da za taso gobe daga kasar Amurka kuma za ta musanya Dalar Amurka dubu 10 da Naira. “Washegari sai suka zo suka hada baki da wani mutum da ke aiki a bankin GTB a nan yankin Ikurodu, suka kira dan uwana Alhaji Yakubu Musa wanda yayana ne uwarmu daya ubanmu daya tare da abokin kasuwancinsa Alhaji Hassan Umaru, inda suka je bankin GTB suka iske mutanen suka biya kudin Dala Amurka Dubu 10 a asusun da suka ba su a bankin. Wato Naira miliyan 3 da doriya bayan suka biya kudin sai mutanen suka ce musu su fito su karbi Dalar a waje a cikin motarsu, suna isowa wajen sai suka nuna musu bindiga suka tursasa su suka shiga motar, daga nan suka tafi da su. Wannan ne bayanan da jagoran masu garkuwar ya yi wa ‘yan sanda ke nan a lokacin da aka kama shi ake yi masa tambayoyi,” inji shi.

Alhaji Munkaila Musa ya ce a ranar da masu garkuwa da mutanen suka tafi da ’yan uwansu sai suka kira su ta wayar salula suka sanar musu cewa sun yi garkuwa da ’yan uwansu don haka su turo Naira miliyan daya da dubu 600.

“Nan da nan muka hada kudin muka kira su muka tambaye su a ina za su karbi kudin sai suka ba mu lambar asusun banki muka tura musu kudin amma ba su sako su ba, sai muka sanar da ’yan sandan SARS wadanda suka yi ta bibiyar lamarin tun daga wancan lokaci suka kuma yi sa’ar kama jagoran masu garkuwar bayan sun kama mai asusun bankin wacce budurwarsa ce. Jagoran nasu ne ya ba da bayanan da aka kama ma’aikacin bankin da karin mutum guda yanzu saura mutum 3 da ake farautarsu. Da farko jagoran nasu ya shaida wa ’yan sanda cewa ’yan uwanmu suna nan amma yanzu ya tabbatar musu cewa shi ne ya kashe su, kuma ya rufe su a wani rami. Yanzu haka ’yan sandan na SARS suna cigaba da bincike, suna kokarin kamo ragowar wadanda ake zargi kafin su je a tuno gawarwakin,” inji shi.

Shugaban Kungiyar Matasan Arewa na Jihohin Kudu maso Yamma, Kwamared Ya’u Alhaji Musa Sakaba da ke fadi-tashi kan lamarin ya shaida wa Aminiya cewa ga dukkan alamu wadanda ake zargin ’yan kungiyar asiri ne ba masu garkuwa da mutanen da aka saba ji ba wadanda suke kama mutum don karbar kudin fansa ba. “Ka san yankin Ikorodu yanki ne da ya tara matsafa da ’yan kungiyar asiri don haka muna kyautata zaton wadanan mutane su ne, sun kashe mana mutum biyu manyan mutane masu dukiya da suke hada-hada a nan Kasuwar ‘Yan canji ta Ikorodu, Alhaji Hassan  Umaru mai shekara 37 ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 10, maza 4 mata 6 da Alhaji Yakubu Musa wanda ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 11 maza 8 da mata 3. Yanzu haka iyalansu na cikin zullumi da fargaba da tashin hankali. Ya kamata gwamnati ta yi azama wajen dakile irin wadannan masifu,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya ce rundunar ba za ta ce komai a kan wannan lamari ba, saboda tna ci gaba da bincike ne a kai tukunnna.