✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake bikin Maulidi a sassan Najeriya

Al’ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da shagulgulan Maulidi a matsayin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad, Tsira da Amincin Allah su…

Al’ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da shagulgulan Maulidi a matsayin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah, Annabi Muhammad, Tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

A Najeriya, Gwamnati ta ware ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutun Maulidin bana, wanda ya yi daidai da 12 ga watan Rabi’ul Awwal a Kalandar Musulunci.

A bana, yawancin jihohi na bikin Maulidin ne daga safe zuwa yammaci maimakon yadda aka saba yi a cikin dare saboda dokar takaita lokutan fita da aka sanya a wasu jihohin sakamakon rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar #ENDSARS.

Aminiya ta samo hotunan yadda bikin Maulidin ke gudana a jihohin Kaduna da Gombe.

Wani bangare na masu zagayen Maulidi a Jihar Gombe
Dandazon masu zagayen Maulidi a Jihar Gombe.
Wani sashe na masu zagayen Maulidi a Jihar Gombe
Wasu daga cikin masu zagayen Maulid a Jihar Gombe.

Wani sashe na mahalarta taron Maulidi na Bana a Kaduna

Yan agajin kungiyar Fityanu a wajen hawan Maulidi a Jihar Gombe.