✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake cincin mai kama da kek

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan lokaci uwargida, tare da fatan an yi Sallah lafiya. Mata da dama ba su iya amfani da…

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan lokaci uwargida, tare da fatan an yi Sallah lafiya. Mata da dama ba su iya amfani da fulawa wajen sarrafa ta wajen yin kayan marmari ba. Da yawan mata sun fi kwarewa ne a harkar girke-girken da ake yin su da albasa da kayan miya. Ganin hakan ne y asa a yau na kawo muku yadda ake yin cincin mai kama da kek.  Tare da fatan za a gwada a gida domin sanya kunnuwan maigida su yi motsi.  A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata:

• Fulawa

•Suga

• ‘Baking powder’

•Butter/ man gyada

•kwai 15

Hadi:

Da farko dai, za a samu kwano ko roba sannan a fasa kwai guda goma sha biyar a ciki. Bayan haka sai a samu kofi tsaka-tsaki a auno suga daidai girman wannan kofi sannan a zuba a cikin ruwan kwan  a yi ta gaurayawa har sai ta narke. A sake dauko wannan kofin da aka auna suga a narkar da ‘butter’ sannan  a zuba a kofin har sai ya cika sannan a zuba a cikin hadin suga da kwai a cigaba da motsawa da muciya,  sannan a debo ‘baking powder’ babban cokalin cin abinci daya ya cika sosai sannan a zuba. A cigaba da gaurayawa. A sake debo fulawa daidai cikin wannan kofin da aka auno suga da sauransu a auno fulawa kofi daya sannan a zuba a cikin hadin a cigaba da juyawa . Idan  hadin ya yi ruwa-ruwa sai a dan kara fulawa kadan ta yadda in an sanya hannu ba zai manne ba. Amma kada a bar fulawar ta yi taurin hadin cincin din da aka saba.

A wanke hannu a goge sannan a gutsuro wannan kwabin  a danna a tafin hannu a mulmula sannan a yi masa rami a tsakiya kamar awarwaron da yara mata ke sanya wa a hannu, sannan a dora man gyada a kan wuta a soya. A bar shi a kan wuta domin hadin ya soyu daga nan sai a soke.

Za a iya cin irin wannan cincin da  shayi da kuma lokacin da za a tarbi baki.