✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dahuwar kaza ’yar China

Assalamu alaikum uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani sabon salon dahuwar kaza ’yar China. Tare da fatan…

Assalamu alaikum uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani sabon salon dahuwar kaza ’yar China. Tare da fatan uwargida za a gwada irin wannan ga maigida koda sau daya ne a wata. Ina son a sani cewa canja salon girke-girke na hana mutum cin girki iri daya. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Namankaza zalla marar kashi
  • Albasa
  • Abarba
  • Garin masoro
  • Ridi
  • Barkono
  • Magi
  • Man gyada
  • Tafarnuwa
  • Soy sauce (ana samu a kantunan sayar da abincin zamani)
  • Binegar
  • Ketchup

Hadi

Bayan an wanke kazar sannan a yanyanka ta kanana. Bayan haka, a zuba garin masoro da magi sannan a ajiye a gefe. A dora tukunyar tuya a wuta sai a zuba man gyada kadan sannan a dauki wannan naman kazar a rika soyawa har sai ya yi launin kasa-kasa irin na soyuwa. Sannan a kwashe a ajiye a gafe.

A wannan tukunyar tuyar sai a zuba man gyada kadan da yankakkiyar albasa sannan a zuba soyayyiyar kazar a ciki ana gaurayawa na tsawon minti daya.

A samu wani kwano sai a zuba soy sauce din da wannan kazar a sake kwaba su. Bayan haka, a zuba ruwan abarba da barkono da garin tafarnuwa har sai sun nuna sannan a sauke.

Za a a iya hada wannan girki da jus mai sanyi. A ci dadi lafiya!