✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza

Barkanmu da warhaka uwargida da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza.…

Barkanmu da warhaka uwargida da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza. Wannan irin dahuwar ana yi wa maigida ne a lokacin da zai dawo daga tafiya. Bugu da kari, domin burge maigida yin irin wannan girkin shi ya fi cancanta. Da zarar mace ta iya girki, zai yi wuya a ga maigida yana cin abinci a waje koda a gidan biki ne zai gwammace ya dawo gida yaci na uwargidansa. Don haka sai a dage mata!

Kayan hadi

•        Nikakkiyar kaza

•        Garin burodi

•        kwai

•        Fulawa

•        Attarugu

•        Garin tafarnuwa

•        Magi

•        Kori

•        Garin citta

•        Masoro

Yadda ake hadin

Uwargida ta samu kaza ta cire kashin jikin kazar sannan ta nika ta. Bayan ta nika, sai ta zuba a kwano. Sannan ta zuba dakakken masoro da kori da garin citta da magi da garin tafarnuwa da dakakken attarugu sannan ta cakuda su sosai.

Bayan an yi haka, sai a mulmula hadin sannan a sa a cikin fulawa sannan a sake shafa mata garin burodi sannan sai a zuba ruwan kwai sannan a jefa a man gyada mai zafi a tukunyar tuya. Bayan ta soyu sai a tsame. 

A ci dadi lafiya.