✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dahuwar shinkafa ’yar Senegal

Asalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa ’yar Senegal. Wannan shinkafar dai ba…

Asalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa ’yar Senegal. Wannan shinkafar dai ba wata shinkafa ba ce illa shinkafar da aka saba dafawa a gida amma yadda ake sarrafa ta daban yake da yadda ake sarrafa shinkafa dafa-duka ko fara ko soyayyiyar shinkafa. Domin sake kwarewa dangane da sarrafa nau’o’in girke-girke, a juri karanta jaridar Aminiya bangaren girke-girke a kowane mako.

 

Abubuwan da ake bukata

  • Shinkafa
  • Karas
  • Koren wake
  • Tattasai
  • Attarugu
  • Albasa
  • Nikakken nama
  • Magi
  • Kori
  • Garin tafarnuwa da citta

Hadi

A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa sannan a dauko shinkafa ’yar wara a wanke a zuba a ciki. Idan ta dan tafasa kamar na minti10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da  ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane. Sannan a samu danyen nama a nika shi. Naman ya kasance da dan yawa.

A sake dora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyada a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai. Sannan sai a zuba nikakken naman a ciki a ci gaba da soya shi sannan a dauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a sauke.

A samu salad a yayyanka a dafa kwai a zuba ‘cream` sannan a dora a ci, ita da jus din lemo.

A ci dadi lafiya.