✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake fafata Gasar Firimiyar Najeriya ta bana

A ranar Lahadi ce aka fafata wasa na 18 a Gasar Firimiyar Najeriya na bana, duk da cewa akwai kungiyoyin da suke da kwantan wasa,…

A ranar Lahadi ce aka fafata wasa na 18 a Gasar Firimiyar Najeriya na bana, duk da cewa akwai kungiyoyin da suke da kwantan wasa, wato sun buga wasanni 17 ke nan maimakon 18.

Kungiyar Plateau United ce ke kan gaba, inda take saman reburin gasar da maki 32 a wasanni 18, sai kungiyar Lobi Stars na Makurdi ke biye mata da maki 31 a wasanni 17, ke nan idan ta buga kwantan wasanta, ta yi nasara za ta koma ta daya, idan kuma ta yi kunnen doki, za ta yi kunnen dokin maki, sai kuma bambancin zura kwallaye ko yawan kwallayen da aka zura a ragarsu ta bambance su.

Kungiyar Rivers United ce ta uku da maki 29 bayan wasanni 18.

A kasan tabur din kuma, Adamawa United ce ke karshe da maki 14 bayan wasa 18, sai kungiyar Enyimba na Abia ke na kusa da karshe da maki 15 a wasanni 12, sai Rangers United ita ma mai maki 15 a wasanni 12, sai kuma Nasarawa United mai maki 16 a wasanni 17.

Teburin Gasar Firimiyar Najeriya a yanzu haka Hoto: LMC

Kungiyoyin Enyimba da Aba da Rangers United sun buga wasanni 12 ne kawai dukkansu a cikin wasanni 18, wanda hakan ya sa suka yi kasa matuka.

Ke nan suna da kwantan wasanni 6, wanda ta yiwu bayan wasannin yanayin teburin ta canja zani.

A da can, a Gasar Firimiyar Najeriya, abu ne mai wuya a wata kungiya ta samu maki a gidan wata, ballanata ma har a doke wata kungiya a gidanta.

Amma a kakar bana na gasar, an samu sauye-sauye da dama, inda ake zuwa har gida a doke kulob, ko kuma a zo har gidansu a samu maki, wato a yi kunnen doki.

A wasanni na 18 da aka fafata, kungiyar Dakkada FC ta yi kunnen doki a gidan Wikki Tourist na Bauchi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa.

Haka ma a Jihar Anambra, kungiyar Akwa United ta rike kungiyar Ifeanyi Ubah a gidan, inda aka tashi wasan da kunnen doki.

Haka ma a wasa na 17, an samu kunnen doki guda uku a wasanni daban-daban.

A wasanni na 16, an samu kunnen doki da dama, sannan kuma kungiyar Warri Wolves ta doke Nasarawa United da ci 2 da 1 a gidan Nasarawa United.

Haka aka rika samu a wasannin baya, inda aka rika samu sakamakon bazata a gasar.

Wasan tsakanin Rivers United da Wikki Tourist a Port Harcout Hoto: LMC

Yanzu kallo ya koma sama, inda Plaeau United ke ta kokarin ci gaba da kasancewa a saman teburi, domin lashe gasar, sannan kuma Lobi Stars na ci gaba da matsa mata lamba.

Sannan kuma akwai Enyimba da Rangers United da yanzu suke karkasin taburi, amma duk lokacin da hankalinsu ya dawo gasar, suka buga wasanninsu da suka rage, ana iya samun canjin bazata.