✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake fafata Kofin Zaman Lafiya na Yariman Jere

A makon jiya ne aka fara fafatawa a Gasar Kofin Zaman Lafiya na Yariman Jere, wanda aka shirya karkashin Kungiyar wasan kwallon kata ta Jere, wato…

A makon jiya ne aka fara fafatawa a Gasar Kofin Zaman Lafiya na Yariman Jere, wanda aka shirya karkashin Kungiyar wasan kwallon kata ta Jere, wato Jere football Association (JEFA).

Yariman Jere Alhaji Abdulkareem Suleiman ne ya dauk nauyin gasar, wanda aka fara a ranar 22 ga watan Fabrailun.

Ranar farko na gasar ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Jere, ciki har da Yariman Jeren da Kwamandan rundunar tsaron farin kaya na yankin, shugaban ’yan sanda na yakin Umar Faruk ma ya halarta da kwamnadan soja da Turakin Jere Alhaji Abubakar Tanko da Shamakin Jare da wakilin Watsa Labaran Jere da sauransu.

Shi dai wannan kofin an shirya shi ne domin samun zaman lafiya a tsakanin matasa da kuma habaka harkokin wasanni.

Kwamitin tsare-tsaren wasan su ne, Salisu Musa Jere da Shehu Shagari da Alhaji Musa Ibrahim.

A yau Juma’a za a fatata wasa ne tsakanin kungiyar Young Boys FC da AS Roma Unguwar Iya.

Alhaji Abdulkareem Suleiman Yariman Jere wanda shi ne Shugaban Kungiyar Jere football Association (JEFA), wanda kuma shi ya assasa tare da daukar nauyin wannan gasa, ya ce irin wannan gasa zai taimaka wajen kara samun hadin kai tsakanin matasa da taimakonsu wajen bunkasa harkokin wasanni.