✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake gashin nama a Obin (Oben)

Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Yaya shirin Sallah? Tare da fatan za a yi kokarin gwada akalla daya daga…

Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Yaya shirin Sallah? Tare da fatan za a yi kokarin gwada akalla daya daga cikin girke-girken da muke kawo muku. A yau na kawo muku yadda ake gashin nama a obin saboda Sallah da ke gabatowa ko za a gwada irin wannan gashin kuma domin girka nau’o’in girki da dama domin burge maigida da kuma manyan gobe.

Abubuwan da za a bukata

  • Nama
  • Madara
  • Albasa
  • Lawashin albasa
  • Tafarnuwa
  • Gishiri
  • Garin masoro
  • Barkono
  • Man Zaitun
  • Kwai

Hadi

A kunna Obin ya yi zafi, sannan a samo kwano a kwaba madara sai a zuba garin masoro da jajjagen tafarnuwa da garin barkono da gishi da lawashin albasa sannan a gauraya sosai. Bayan haka sai a tsoma naman a cikin hadin sannan a zuba sauran hadin a cikin tire din Obin sannan a dora naman a ciki. Sannan a dauko dafaffen kwai a bare a yanka shi sai a saka a gefen naman. Sai a gasa na tsawon awa daya sannan a sauke a jira ya huce kafin a fara ci. A ci dadi lafiya.