✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka alalen manja

Barka da warhaka Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake hada alalen manja. Akwai hanyoyi…

Barka da warhaka Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake hada alalen manja. Akwai hanyoyi da dama kan yadda kowace mace take girka nata alelen manjan. Yadda wata za ta girka nata daban yake da yadda wata za ta girka. Don haka ne a yau na kawo muku irin namu salon dahuwar alelen manja koda akwai wadda take bukatar gyara ta dauki darasi daga ciki. 

Abubuwan da za a bukata

• Wake

• Manja

• kwai

• Attarugu

• Magi

• Tattasai

• Albasa

• Hanta

• Garin kifin cryfish

• Kori

Hadi

A samu wake sai a jika shi sannan a dan jajjaga shi sama-sama a cikin turmi. Sai a wanke shi a cire hancin waken har sai ya yi fari sal. Sai a zuba attarugu da albasa da tattasai a kai sannan a kai inji a markada shi ya yi laushi.

A samu kwai a dafa shi a yanyanka shi kanana a ajiye a gefe. A dafa hanta ita ma sai a yanka kanana a ajiye a gefe. A zuba magi da kori da yankakkiyar hanta da kwai da garin kifin cryfish da manja ko man gyada. Sannan a gauraya su sosai har sai sun hadu. Sannan a sami leda santana ko gwangwani  a zuba kullin da ludayi sannan a daure. Ko kuma in a gwangwani ne, sai a zuba mai a gwangwanin kafin a zuba kullin a ciki.

A dora ruwa a tukunya ya tafasa kafin a sanya ledar kullin ko gwangwanin a cikin ruwan sai a rufe da marufi. Bayan awa daya, sai a sauke. Za a iya buda baki da irin wannan alale musamman in an hada shi da kunun shinkafa ko na alkama.