✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka burabusko da miyar taushe

Barkanmu da sake saduwa da ku iyayen gida a wannan fili namu na girke-girke. Kamar yadda ake cewa taba kidi taba karatu, haka kuma aka…

Barkanmu da sake saduwa da ku iyayen gida a wannan fili namu na girke-girke. Kamar yadda ake cewa taba kidi taba karatu, haka kuma aka ce duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka nake ganin ya kamata mu koma gargajiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar taushe da burabusko da man shanu. Tare da fatan za a rika gwada wa maigida. A sha karatu lafiya.

 

Abubuwan da ake bukata

  • Garin burabusko
  • Alayyahu
  • Nikakkiyar gyada
  • Magi
  • Kori
  • Garin tafarnuwa
  • Man shanu
  • Tantakwashi
  • Manja
  • Attarugu
  • Albasa da tumatir

 

Hadi                                                                       

A dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai a rage wutar sannan a zuba garin burabusko ana gaurayawa sai a rufe da marufin tukunyar. A sake rage wutar sannan a jira kamar na tsawon minti 20. Sannan sai a kwashe da mara a sa a kwano a ajiye a gefe.

A silala nama da tantakwashi da albasa da gishiri kadan. Bayan haka, sai a jajjaga tumatir da attarugu. A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja idan ya yi zafi sai a zuba albasa idan albasar ta soyu sannan a zuba wannan jajjagaggen kayan miyar. A yi ta juya su har sai sun soyu.

A dauko nikakkiyar gyada a dama sannan a zuba romon naman da silalen tantakwashi a cikin kayan miyar. Bayan haka, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa sai a gauraya. Idan ya dan tafasa, sai a zuba kwababbiyar gyadar nan a cikin hadin kayan miya a sake gaurayawa.

A yayyanka alayyahu sannan a wanke da ruwan gishiri domin wanke datti da cututtukan da ke cikin ganyen. Sai a wanke kamar ruwa uku. A koma a sake juya miyar a kan wuta.  A jira gyadar ta nuna sosai sannan a zuba wankakken alayyahu a rufe.

Bayan minti biyar, sai a sake gauraya miyar. Sai a sauke a dauko man shanu a soya da albasa sannan   a zuba a kan miyar. Girki ya nuna! A dauko tuwon burabuskon nan a zuba masa wannan miyar a kai. A bai wa maigida.

A ci dadi lafiya!