✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka farfesun Indomie mai kifi

Barkarmu da warhaka Uwargida. yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku sabon salon girka taliyar Indomie. A shekarun…

Barkarmu da warhaka Uwargida. yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku sabon salon girka taliyar Indomie. A shekarun baya idan ba a manta ba na taba kawo muku wani salon girka Indomie wadda ake wanke shi kafin a zuba kayan hadi. A yau na kawo muku yadda ake yin farfesunsa da kifi danye, tare da fatan za a dauki darasi kuma a gwada a gida don manyan gobe.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Kifin karfasa/tarwada

•        Indomie

•        Attarugu

•        Albasa

•        Tafarnuwa

•        Ganyen kori

•        Magi

•        Kayan kanshi na girki

•        Karas

•        Lawashi

 

Hadi

Da farko za a wanke kifin yadda karnin zai fita sosai. Za a iya wankewa da ruwan kanwa ko toka domin rage karninsa. Bayan haka sai a zuba a tukunya sannan a zuba yankakkiyar albasa da jajjagen tafarnuwa da attarugu da magi sannan a zuba ruwa a cikin hadin.

Sai a dora a kan wuta a jira har sai kifin ya nuna sosai sannan a dauko taliyar Indomie a yi mata tafasa daya, sannan a dauraye da ruwan sanyi a tsane ta sosai sannan a zuba a cikin farfesun kifin, sannan a zuba  yankakken karas a ciki da lawashi da kuma ganyen kori.

Bayan ’yan mintuna kadan sai a sauke daga kan wutar a zuba a cikin kwano kamar na cikin kwanon.

A ci dadi lafiya!