✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar koda

Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana nan  lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar koda. Akwai hanyoyi da dama…

Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana nan  lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar koda. Akwai hanyoyi da dama da mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a rika karanta wannan shafi domin gano sirrikan girki da kuma canja salon girki a koyaushe domin yara su rage kwadayi a makwabta.

Abubuwan da za a bukata

  • Koda
  • Albasa
  • Tumatir
  • Garin tafarnuwa
  • Magi
  • Kori
  • Garin citta
  • Attarugu
  • Man gyada
  • Koren tattashi

 

Hadi

A wanke koda ta fita fes. Sannan a yayyanka ta kanana sai a sanya ta a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a rufe. Idan ta fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki a zuba yankakken tumatir da magi da garin tafarnuwa da garin citta kadan. Sannan a rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a ci gaba da juyawa har sai albasa da tumatir da attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a kwano. Sai a yayyanka danyar albasa da koren tattashi a zuba a kan kodar domin kawata girkin.

Za a iya cin wannan girki da dafa-dukar shinkafa ko kuma farar shinkafa da jus din lemun zaki.

A ci dadi lafiya.