✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar ‘Oha’

Assalamu alaikum Uwargida, tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau mun kawo muku girkin bangaren Ibo wato miyar ‘Oha’. Wannan miyar gargajiya ce…

Assalamu alaikum Uwargida, tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau mun kawo muku girkin bangaren Ibo wato miyar ‘Oha’. Wannan miyar gargajiya ce wadda suke yin ta a gidanjensu da ganyen ‘Oha’ wanda a wajensu ake samun wannan ganye. Domin mazauna Arewacin Najeriya za a iya zuwa kasuwa a duk inda suke sai a tambaye su wannan ganyen za su ba da. Sai dai ganyen lokaci-lokaci ake samunsa. Za a kuma iya amfani da ganyen shuwaka wajen sarrafa wannan miyar idan babu na oha din.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Ganyen ‘Oha’

•        Gwaza kanana kamar guda takwas

•        Manja kamar cokali uku

•        Naman shanu

•        Kayan ciki

•        Kifi banda

•        Busashen kifi

•        Borkono

•        Magi

•        Kifi ‘Cryfish’

Hadi

A dafa kayan ciki da busasshen kifi da bandar ta yadda za su yi laushi sannan a wanke naman shanu a zuba a tukunyar da kayan cikin ke ciki da sauran kifin. A ci gaba da dafa su har sai naman ya nuna sannan a zuba magi kamar guda biyu sannan a ci gaba da dafawa har na tsawon minti biyar.

Sannan a zuba dakakken borkono da dakakken ‘cryfish’ sai a ci gaba da dafa su na tsawon minti goma sannan a tafasa gwaza sannan a kwaba ta a ruwa kadan a zuba .

A ci gaba da dahuwar sannan a zuba manja a rufe tukunyar har sai miyar ta dan yi kauri. Za a iya kara ruwan zafi idan miyar ta cika kauri sannan a gauraya sai a tsinka ganyen Oha da hannu kuma a yanka shi da hannu ba da wuka ba domin kada ganyen ya yi baki sannan sai a gauraya.

Za a iya cin wannan girki da sakwara ko tuwon samobita da sauran nau’ukan tuwo.  A ci dadi lafiya!