✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar shuwaka

Assalamu alaikum Uwargida! Barkanmu da sake saduwa  daku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara  cewa…

Assalamu alaikum Uwargida! Barkanmu da sake saduwa  daku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara  cewa miya ita ce sirrin dadin abinci ba. Idan har mace ta iya sarrafa miya da dama, lallai kakarta ta yanke saka. Domin maigida ko tafiya zai yi sai ya yi marmarin yin tafiyar da ita. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake miyar shuwaka, tare da fatan za a gwada irin wannan girki don kwarewa a fanin girke-girke.

Abubuwan da za a bukata

•        Ganyen shuwaka

•        Manja

•        Jan nama

•        Kayan ciki

•        Kifi banda

•        Danyen kifin karfasa

•        Magi

•        Kori

•        Kifin ‘cryfish’

•        Attarugu

Hadi

A cire fatar danyen kifi karfasa sannan a dora a wuta hade da magi da ruwa a dafa har sai ya yi laushi sosai sannan a sauke. A cire kashin kifin gaba daya, sannan a zuba a turmi a daka shi har sai ya yi laushi sannan a kwashe a ajiye a gefe.

A wanke naman da kayan ciki a dora ak an wuta da gishiri kadan. Sannan a wanke bandar kifin a cikin ruwan zafi a cire kayar kifin.

Bayan naman da kayan cikin sun nuna sannan a zuba su a cikin tukunya tare da bandar kifin da kifin ‘cryfish’ da kuma dakakken kifin karfasar. Sannan a dauko wankakkiyar shuwaka a dora a kan wuta da jajjagen attarugu da kori.

Sannan a gauraya su a zuba magi da manja. Idan ganyen shuwakar ya nuna a sai a sake gauraya girkin a sauke.

Za a iya hada wannan miya da kowane irin tuwo. A ci dadi lafiya!