Search
Subscribe
Yadda ake girkin  ‘meat beggie’

Yadda ake girkin  ‘meat beggie’

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A wannan mako na kawo muku wani nau’in girki irin na Turawa domin samun canji game da irin girke-girken da muke yawaita su a gida. Koyon sabon abu a kullum na kara fasaha da gwanancewa, don haka dole ne uwargida ta kasance mai koyon nau’o’in girki da dama na gida Najeriya da na kasashen waje domin wayar da kan manyan gobe da kuma sabar musu da cin irin wadannan girki.

Abubuwan da za a bukata

•        Nama

•        ‘brocolli’

•        Tafarnuwa

•        Citta

•        Sukari/zuma

•        Attarugu/ yaji

•        ‘Dark soy sauce’

•        Man zaitun/ ridi

•        Fulawa

Hadi

A yayyanka nama kanana. Sannan a yayyanka brocolli kanana. A dora tukunya mai kyau a wuta wadda ba ta kona abinci (non-stick) sannan a zuba man zaitun kadan sai a dauko yankakken naman a zuba a ciki tare da barbada masa gishiri da dan yaji ana gaurayawa har sai ya nuna sannan a kwashe. A sake zuba man zaitun a tukunya a dauko yankakken brocolli a zuba tare da sanya dan gishiri da yaji har sai ya nuna sannan a sauke.

A dora tukunya a kan wuta. Sannan a zuba man zaitun kadan sai a zuba yankakkiyar tafarnuwa da citta a soya su sannan a dauko dark soy sauce din a zuba tare da zuba zuma da ruwan silalen nama da kuma fulawa kadan. Sai a gauraya su har sai miyar ta yi kauri. Sannan a dauko wannan naman a zuba tare da broccolli a zuba a gauraya sannan a samu farar shinkafa a dora a kai. A ci dadi lafiya.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin