Search
Subscribe
Yadda ake hada ‘Chiken Culet’

Yadda ake hada ‘Chiken Culet’

Barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke. Da fata uwargida ta gwada  girkin da muka yi a makon da ya wuce. Ya kamata a rika kokartawa domin sanya kunnen maigida motsi. A yau mun kawo muku wani salon girki mai suna ‘Chiken Culet.’ A rika  gwada girke-girken da muke kawo muku domin kwarewa a harkar girki.

Abubuwan da za a bukata

• Nikakken naman kaza (minced meat)

• Busasshen burodi (bread crumbs)

• Kwai

• Magi da gishiri

• Tooth pick

 

Hadi

Idan kin samu nikakken naman kaza, sai ki fasa kwai da busasshen burodi da gishiri da magi, ki hada su sosai amma kada ki bari ya yi ruwa. Bayan haka, sai uwargida ta sake fasa kwai ta kada shi a kwano. Sai ta saka hadin kuma a cikin busasshen burodin (nikakke). Sai ki dunkule shi ko ki yi shi ya zama falai-falai, kisa a toothpick. Za ki iya sanya shi a firiji idan ba ki da niyyar soya shi a lokacin. Sai ki soya shi a man gyada mara yawa. Hmmn..!! lagwada! Lallai girkin nan sai ya sanya maigida manta agogonsa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin