✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada gasasshiyar kaza da dankali

Assalamu alaikum warahamatullah, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili namu na girke-girke. Uwargida a yau na kawo yadda ake hada girkin gasasshiyar kaza…

Assalamu alaikum warahamatullah, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili namu na girke-girke. Uwargida a yau na kawo yadda ake hada girkin gasasshiyar kaza da dankali. Da fatan ana karuwa da abin da muke kawo muku na nau’o’in girke-girke.

 

Kayan hadi:

•    Kaza

•    Dankali

•    Man gyada

•    Barkono

•    Kayan kanshi

•    Magi

•    Tafarnuwa

•    Gishiri

•    Kori

•    Ganyen fasili

Yadda ake yi:

Idan uwargida kika samu kazarki sai ki yanyanka ta sannan ki wanke. Daga nan sai ki zuba mata mangyada ki kawo kayan kanshi ki zuba a kai sai ki kawo jajjagaggiyar tafarnuwa ki zuba. Sannan ki zuba barkono da garin kori, sai ki cuccuda naman kazar nan don kowa ne nama ya cudanya da kayan hadin nan na dandano. Daga nan sai a ajiye kamar awa biyar ko kuma a yi hadin tun dare a sa shi a firiji. Hakan shi zai sa kayan hadin su shiga jikin naman sosai.

Daga nan sai ki dauko dankalin Turawa ki raba shi kamar hurhudu sannan sai ki dafa shi da ruwa sama-sama sannan ki sauke ki zuba shi a cikin naman kazar nan ki ajiye a gefe. Sai ki dauko farantin gashi ki zuba naman kaza da dankalin nan a ciki sannan ki dauko ganyan fasili ki zuzzuba a kai don kwalliya. Sai ki sanya shi a cikin Oben ki bar shi ya gasu zuwa minti 30. Idan ya gasu sai a fito da shi a ci.