✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada kazar ‘chicken balls’

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Masu karatunmu da dama na ta tura mana sakonnin cewa a sake yi musu bayani kan…

Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Masu karatunmu da dama na ta tura mana sakonnin cewa a sake yi musu bayani kan wannan girki na ‘chikin balls.’ Don haka a yau na sake kawo muku yadda ake hadawa tare da fatan za a sa ido domin ba mu cika son komawa baya ba. Domin kada wani girki ya wuce ki, sai a ci gaba da sayen jaridar Aminiya a kowace juma’a. A sha karatu lafiya.

 

Kayan hadi

  • Kaza
  • Kwai
  • Dankalin Turawa
  • Magi da gishiri
  • Tattasai da attarugu da albasa
  • Man gyada
  • Kori ‘Curry’

 

Hadi

Idan uwargida ta wanke kazarta tas, sai ta tafasa ta da dan gishiri da albasa har sai ta yi laushi sosai, sannan a cire kasusuwan da ke jikin kazar. A dafa dankalin Turawa ya dahu sosai sannan a ajiye shi a gefe. A markada tattasai da attarugu da albasa. Bayan haka, sai a tsoma dafaffen dankalin tare da kazar a cakuda su da magi da gishiri da kuma curry. Sannan a fasa kwai a kan hadin da aka yi. Sai a mulmula su daya bayan daya. Sannan a dora man gyada a wuta a tukunyar tuya a soya su. Bayan sun soyu sai a sauke.

Himm dadi! Wannan irin girkin ba a bai wa mai kyuya. Za a iya cin wannan girki da safe.