✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada kosan ojojo

Barkanmu da warhaka uwargida. Ko kun san mene ne kosan ojojo? Wannan wani irin salon girki ne na kosan doya. Ana yin sa ne domin…

Barkanmu da warhaka uwargida. Ko kun san mene ne kosan ojojo? Wannan wani irin salon girki ne na kosan doya. Ana yin sa ne domin samun abin karyawa da safe kuma ba ya da wani mahadi illa kunu ko shayi. Ya kamata ana canja wa maigida salon girki domin hana shi zuwa gidan abinci don cin abinci.

 

Abubuwan da za a bukata

  • Doya
  • Kwai
  • Abin nika doya (grater)
  • Citta
  • Magi
  • Albasa
  • Attarugu
  • Man gyada
  • Curry

 

Hadi

Bayan uwargida ta fere doyarta, sai ta samu abin kankare karas (grater) sai ta rika nika doyar da shi. Idan ta gama, sai ta jajjaga attarugunta (idan ita mai son cin yaji ne) ta yayyanka albasa kanana ta zuba curry. ta fasa kwai a cikin hadin da magi da kuma garin citta. Sannan sai ta kwaba hadin.

Ta dauko man gyadanta ta dora a kan wuta a tukunyar tuya. Idan ya yi zafi, sai ta dan zuba albasa a man sannan sai ta rika diban kwabin da ta yi tana jefawa a cikin tukunyar tuya kamar yadda ake yanka kosai a man gyada.

Idan gefe daya ya soyu, sai ta sake juya kosan ojojo ta daya gefen domin shi ma ya soyu. Sannan sai ta tsame a matsami.

An fi son cin wannan girki da safe. Kuma za a iya hada wannan girki da kunu ko koko ko kuma shayi domin samun gamsuwa. Lallai wannan girki na sanya kunnen maigida motsi. Hmmn!