✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hadin ‘Ardeb’

Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba.…

Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri. A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi. Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da ake bukata
•Tsamiya
• Siga
•Masoro
• Kanamfari
•Citta
• Ruwa
Hadi
A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai.
dayan hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace. A dora tukunya a wuta bayan tukunya tayi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Hadin ‘ardeb’ ya hadu. A sha lafiya.