✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kosan burodi da kwai

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Mata da dama akwai hanyoyi da suke bi wajen yin kosai. Sai dai…

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Mata da dama akwai hanyoyi da suke bi wajen yin kosai. Sai dai yadda wata za ta sarrafa nata kosan daban yake da yadda wata za ta sarrafa nata. Wadansu bayan sun markada wake sai su fasa kwai a ciki sannan su soya. Kamar yadda nake ba da shawara a baya cewa yana da kyau a koyi nau’o’in girki domin sanya kunnen maigida motsi a koyaushe. A yau na kawo muku yadda ake girka kosan burodi da kwai ne. A sha karatu lafiya.

 

Abubuwan da ake bukata

  • Garin burodi
  • Kwai
  • Attarugu
  • Magi
  • Kori
  • Garin tafarnuwa

Hadi

A samu sabon burodi sannan a guggutsura shi kanana har sai ya bushe sannan a mutsutsuka shi da hannu ya zama garin. Ko kuma za a iya sayen garin burodi a manyan shagunan da ke sayar da kayan abincin zamani. A fasa kwai kamar biyar a ciki sannan a zuba magi. A jajjaga attarugu da tafarnuwa a zuba da kori. Sannan a kwaba su su kwabu sosai.

A samu tukunyar tuya a dora a kan wuta a zuba man gyada da albasa. Bayan man ya yi zafi sai a samu cokali a rika gutsura kullun kamar yadda ake gutsura  kullun kosan wake, ana zubawa a cikin man gyada. Idan daya gefen ya soyu sai a sake juyawa zuwa wani gefen domin ya soyu.  Sannan a sauke.

Za a iya cin wannan kosai da kunu ko kuma shayi da safe domin karin kumallo. A ci dadi lafiya.