✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kula da gashi lokacin zafi

Ba wai kawai lokacin sanyi ne gashi ke bukatar kula ta musamman ba, a lokacin zafi ma ya kamata mata su mayar da hankali wajen…

Ba wai kawai lokacin sanyi ne gashi ke bukatar kula ta musamman ba, a lokacin zafi ma ya kamata mata su mayar da hankali wajen kula da gashinsu musamman ganin lokacin ana fama da gumi wanda gashi ma ba a bar shi a baya ba wajen yin gumi haka kuma idan gumin ya yi yawa shi ke haifar da warin kai.

Idan har ya kasance mace ba ta kula da gashinta a wannan lokaci to babu shakka gashin zai rika yin wari musamman a lokacin da ta shiga rana.

Haka kuma zafi yakan sa mata susar kai wanda hakan ke kawo tujewar kitso cikin kankanen lokaci.

Lura da ire-iren abubuwan da muka kawo a sama da wadansunsu za mu ga akwai bukatar daukar matakai a kan hakan don ganin an zauna cikin kula.

• A yawaita wanke gashi. Wannan ya hada da gyaran gashi wajen yin shamfo ta hanyar yin amfani da man shamfo ko kuma a wanke gashin haka kawai da ruwa da sabulun wankin gashi.

• A  karanta shafa mai a gashi musamman man gashi mai maiko.

• A yawaita yin kitso hakan shi zai sa gashi ya rika samun iska, ma’ana iska ta rika shiga cikin gashin.

• Idan ana zaune a gida a rika bude gashin kai yana shan iska