✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kunun kwakwa

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin filin namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake hada kunun kwakwa. Kamar yadda akwai…

Barkanmu da sake saduwa da ku a cikin filin namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake hada kunun kwakwa. Kamar yadda akwai nau’o’in kunu irin su kunun gyada da kunun tsamiya da kunun aya da sauransu, haka ana kunun kwakwa. Wannan kunun an fi son a yi shi domin tarbar baki ko don karin kumallo. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Kwakwa
  • Shinkafar tuwo
  • Madara
  • Sukari
  • Citta
  • Injin markade (blender).

 

Hadi

Ana son uwargida ta wanke danyar shinkafa kamar wankin gero, sai a sanya mata citta kadan. San nan a kai injin markade a nika. Bayan haka, sai a tace kamar yadda ake tace kamu. A jira ya kwanta. A samu  kwakwa sannan a kankare bayanta har sai ta yi fari tas. Sai a yanka ta kanana yadda za ta iya nikuwa a injin markade (blender)). Idan ta yi laushi sai a samu tukunya a tace a ciki. Sannan a dora ruwan kwakwar a kan wuta. Idan ya tafasa, sai a dama kullun danyen shinkafar nan daidai misali a zuba, sai a ci gaba da gaurayawa har sai ya yi kauri. Sannan a sauke. Idan ya dan huce sai a zuba garin madara da sukari daidai dandano. Kafin a fara sha. Hmmmn! Wannan kunu ba a bai wa mai kiwa.