✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake kwalliyar biki

Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Kasancewar  yadda masu sana’ar kwalliyar fuska suke zabga kudi yana da kyau amaryar gobe ta koyi yadda za ta yi…

Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Kasancewar  yadda masu sana’ar kwalliyar fuska suke zabga kudi yana da kyau amaryar gobe ta koyi yadda za ta yi wannan kwalliyar da kanta ba tare da ta kashe ko sisi ba, kuma yadda koda bayan aurenta za ta iya yin irin wannan kwalliya domin burge angonta a kullum.

Ya kamata fitar da za a yi ta biki tafi ta koyaushe kyau. Saboda duk wadda ta kalli amarya koda sau daya ne ba sai ta tambaya wace ce amaryar ba.

Kayan kwalliya

  • Gazal kalar baki da mai ruwan kasa
  • Eye shadow
  • Hoda
  • Mascara
  • Jambaki (ja, shi ne ake yayi yanzu)
  • Fandesho (foundation)
  • Hodar Blush
  • Gashin ido na roba (faud eyelashes)
  • Ma’askar gira (tweezers)

Ka’idoji  

  • Kafin a fara komai, za ki wanke fuskarki da sabulu marar karfi .
  • A dauko ma’askar gira( tweezer) sai ki aske girarki.
  • Sannan sai a jira fuskar ta bushe. Bayan fuskar ta bushe, sai a shafa mai kadan a fuskar musamman ma in fatar mai gausti ce. In ko fatar mai maiko ce, to ba sai kin shafa mai ba.
  • A shafa hodar fandesho mai launin fata. Sannan a bar ta kamar minti uku. Sannan a samu hoda mai kama da launin fatar sai a shafa a fuska zuwa wuya da kunnuwa Saboda kada launin fuskarki ta bambanta da ta wuya.
  • A samu gazal musamman ma launi mai ruwan kasa (dark brown) sai a zana a girar da aka aske.
  • “Eye shadow” launin kayan da zaki sa sai a shafa kamar iri biyu a kan fatar ido.
  • Kwalli; a shafa a ido sai a samu maskara (mascara) launin shudi (blue) ko baki a gashin fatar ido, ana taje shi.
  • Hodar ‘blush’; a shafa a kumatu.
  • Jambaki; a shafa a lebba. Bayan an yi haka, sai a sake samun gazal mai launin kasa wato (dark brown) a bi lebban bakin da shi. Bayan an gama wadannan abubuwa, za a ga fuskar ta canja sosai.