✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake miyar karas

Barkanmu da sake saduwa a wannan filin namu na girke-girke. Kamar kowane mako muna kawo muku girke-girke iri-iri domin sanya uwargida kwarewa a fannin girki…

Barkanmu da sake saduwa a wannan filin namu na girke-girke. Kamar kowane mako muna kawo muku girke-girke iri-iri domin sanya uwargida kwarewa a fannin girki da kuma burge maigida. A yau mun kawo muku yadda ake dahuwar miyar karas. Na san za a yi mamakin wannan miya. Da yawa daga cikinku za su ce shin wannan miyar za ta ciwu kuwa? Tabbas za ta ciwu musamman ma in aka hada ta da farar shinkafa mai karas da ‘peas’. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Karas
  • Tumatir
  • Attarugu
  • Albasa
  • Ganda
  • Kayan ciki
  • Ganyen kabewa (ugwu)
  • Magi
  • Tafarnuwa

Hadi

Da farko uwargida za ta dafa ganda har sai ta yi laushi sosai yadda cokali zai iya raba ta. Haka kayan ciki ana so su yi laushi sosai. Sannan a sa su a gefe. A yanka albasa dogaye da tumatir sannan a jajjaga attarugu da tafarnuwa. A kankare karas sannan a yanka shi a tsaye. A dora man gyada kadan a tukunya sannan a fara zuba albasa sai tumatir da jajjagen attarugu da tafarnuwa da yankakken karas. A soya su sosai. Sannan a zuba magi a sake juyawa har sai magin ya narke.

A dauko wannan dafaffiyar ganda da kayan cikin a zuba a ci gaba da gaurayawa sannan sai a rufe na tsawon minti biyar sannan a yanka ganyen kabewa (Ugwu) a wanke da ruwan gishiri saboda kwari sannan a yanka su kanana sosai sai a zuba. Amma ba a son ganyen ya yi yawa a cikin miyar.