✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake miyar soyayya (Ifunaya soap)

Assalamu alakum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku miyar kabilar ibo, wato miyar ‘Ifunaya’ wadda ke nufin ‘soyayya’.…

Assalamu alakum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku miyar kabilar ibo, wato miyar ‘Ifunaya’ wadda ke nufin ‘soyayya’. Wannan miya ce ta al’ada wadda ta samo asali daga bangaren Inyamurai sannan ana  yin wannan miyar ce a daren farkon ma’aurata. Shi yasa suka sanya mata suna da miyar soyayya. Wannan miyar dai bata bukatar kayan miya.

 

Abubuwan da za a bukata

• Zuciyar shanu

• Kan busashshen kifi

• Bandan kifi kamar biyu

• Kifin ‘cray fish’

• Agushi

• Manja

• Magi

• Kori

• Ganyen Uziza (za a iya samunsa a kasuwannin yankin)

Hadi

Da farko za a sami zuciyar shanu a wanke sannan a daura a wuta ta yi ta nuna. Sannan a sami tafasashen ruwa a zuba a kan busashshen kan kifi kamar biyu a wanke da gishiri sannan a bude tukunyar da zuciyar shanun ke ciki a zuba. Sannan a dauko bandan kifi kamar biyu in kanana ne amma in manya ne, daya ma ya isa. Sai a wanke da ruwan zafi da gishiri sannan a sake sakawa a wannan tukunyar miyar. Haka za tai ta dahuwa sannan a dauko kifin ‘cray fish’ a wanke sannan a zuba a turmi a jajjaga har sai ya yi laushi sannan a kwashe a zuba a cikin miyar.

A sami nikakken garin agushi a zuba mashi ruwan zafi a kwaba sannan a zuba a cikin miyar tare da manja kadan da magi da kuma kori sannan a dan gauraya a rufe.

A sami ganyen Uziza a wanke sannan a yayyanka shi a wanke a ajiye. Idan agushi ya nuna, sai a dauko wannan ganyen uziza da aka yanka a zuba a cikin miyar a gauraya. Bayan miyar ta nuna sai a sauke.

Za a iya cin wannan miyar da tuwon sakwara ko semo ko tuwon shinkafa ko kuma tuwon masara. A ci dadi lafiya.