Da Dumi Dumi

Yadda ake noman kabeji da rani

Yadda ake noman kabeji da rani
Yadda ake noman kabeji da rani

Aminiya ta samu zantawa da wani manomi da ke noman kabeji dan rani a Kogin Gada da ke Zariya a Jihar Kaduna mai suna Alhassan Sulaiman inda ya bayyana yadda ake noman kabejin kamar haka:                                                                                                                                           

“Noman kabeji wanda ake yi wa ban-ruwa, ko noman rani kamar yadda ake sauran noma haka ake yin sa, sai dai nan da muke namu noman ya sha bamban, domin mu rijiyar burtsatse ce muke amfani da ita saboda konewar rafi ko koginmu.

Don haka in ka yi kaftu sai a ja kwami; tunda dama ka riga ka yi yafi domin sai an yafa irin kafin dashe. Dashen shi ake yi don haka za a shata kwami kafin a yafa taki sai an yi ban-ruwa sannan a zo a yi dashe, kuma kowane kwami ana iya dasa kamar tushe 25 har zuwa tushe 50, ya danganta da girman kwamin. Sannan kabeji yana bukatar feshi kamar sauran amfani sai dai kuma idan lokacin zafi ne to lokacin ne da kwari suka fi samun duk wani amfani. An fi yin feshi a-kai-a-kai amma yanzu tunda akwai sanyi to yin feshin maganin yana da sauki,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa: “Duk lokacin da kabeji ya dauki wata uku ya zama kudi domin ya samu. Haka kuma kabeji a yanzu buhunsa mai kilo 50 ya kai Naira 7,500 sai dai shi ma kamar sauran kayan gwari ne yana hawa da sauka cikin lokaci kankane ba ya da tsayayyen farashi.”

Ya yi kira ga gwamnati ta yi kokarin samar wa masu son yin noman rani domin yadda aikin yake samar wa ire-irensu da matasa aikin yi, kasancewar noma babu abin da yake ba jama’a aiki kamarsa.

ADVERTISEMENT

Haka kuma ya ce suna bukatar  iri da kayayyakin aikin noma na zamani.

Share