✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake salad din dankali

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama da mata ke  yin salad; walau na latas ko…

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Akwai hanyoyi da dama da mata ke  yin salad; walau na latas ko kabeji da makamatansu. Kamar yadda nake bayani a kan canja nau’o’i da salon girke-girke ne saboda kada ya ginshi masu ci. Hakan ya sanya a yau na kawo muku yadda ake hadin salad din dankali. Tare da fatar za a gwada irin wannan hadi a gida. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Dafaffen dankalin Turawa
  • Karas
  • Kwai
  • Sausage ( za a iya samu a manyan shagunan sayar da kayan abincin zamani)
  • Bama
  • Sukari
  • Ruwan lemun tsami
  • Naman kaza

Hadi

A fere dankalin Turawa sannan a tafasa a wuta da dan gishiri kadan. A yayyanka karas kanana a wanke sannan a tafasa shi kamar tafasa daya sannan a sauke. A samu cinyar kaza a sulala ta da kayan kanshi da dandano har sai ruwan ya shanye sannan a soya ta a ajiye a gefe. A tafasa Sausage da ruwan gishiri kadan sannan a soya sama-sama yadda ba zai dade a kan wuta ba sannan a sauke. A yayyanka shi kanana.

A samu kwano a zuba yankakken dankalin Turawa da karas da Sausage da soyayyen naman kazar.

Bayan haka a kwaba Bama a wani karamin kwano da ruwan lemun tsami da sukari sannan a dora a kan hadin dankalin da su karas din.  Za a iya cin wannan salad da dafaffiyyar shinkafa ko a kan dafa-dukar shinkafa. A ci dadi lafiya!