✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake salad din kayan lambu da Dankalin Turawa

Assalamu alaikum Uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya? A yau na kawo muku wani nau’in girki ne kan yadda ake hada salad din…

Assalamu alaikum Uwargida. Tare da fatar ana cikin koshin lafiya? A yau na kawo muku wani nau’in girki ne kan yadda ake hada salad din kayan lambu da Dankalin Turawa. Wannan girki na da armashi sosai kuma yana taimaka wa jiki. Musamman ga wadanda ke son rage kiba za su iya yin wannan girki domin samun gamsuwa a wajen cin wannan girki. Kuma za a iya gwadawa wajen tarbar baki ko kuma girka wa manyan gobe.

Abubuwan da ake bukata

  • Dankalin Turawa
  • Koren wake (green beans)
  • Karas
  • Koren tasshi
  • Albasa
  • Broccoli’kayan kanshi
  • Kayan dandano
  • Man gyada

Hadi

A kankare karas a wanke shi, sannan a wanke koren wake da ruwan gishiri da Broccoli da koren tasshi. A fere Dankalin Turawa sannan a tafasa da gishiri kadan sai a ajiye a gefe.

Bayan haka, sai a yayyanka karas manya-manya a wanke a zuba a cikin tukunya da koren wake da broccoli da gishiri kadan sannan a zuba ruwa shi ma kadan a rufe tukunya na tsawon minti daya sai a sauke.

A zuba man gyada kadan a tukunyar tuya sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken koren tasshi a yi ta juyawa sannan a tsamo hadin broccoli da karas da koren wake a zuba a ciki da kuma Dankalin Turawar a yi ta juyawa.

Sai a zuba kayan dandano da kayan kanshi domin kara wa girkin armashi.

Za a iya cin wannan girki da farar shinkafa ko da dafa- dukanta. A ci dadi lafiya!